Da Dumi-Dumi: An kashe kwamishina, Rabe Nasir, a gidansa da ke Katsina

Da Dumi-Dumi: An kashe kwamishina, Rabe Nasir, a gidansa da ke Katsina

  • Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa gidan kwamishinar Fasaha da Kimiyya na Jihar Katsina sun halaka shi
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun kutsa gidan Dr Rabe Nasir ne bayan sallar la'asar suka bindige shi
  • Kafin ya zama kwamishina, Rabe Nasir ya taba rike mukamin mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari kan Kimiyya da Fasaha

Jihar Katsina - An yi wa kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir kisar glla.

Daily Trust ta rahoto cewa an bindige shi ne a gidansa da ke Fatima Shema Estate da ke birnin Katsina.

Da Dumi-Dumi: An kashe kwamishina, Rabe Nasir, a gidansa da ke Katsina
Rabe Nasir: 'Yan bindiga sun kashe kwamishina a jihar Katsina. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, jami'ai sun cafke mutum daya

Wata majiya wacce ta tabbatar da lamarin ta ce:

"An bindige marigayi Nasir ne bayan sallar La'asar a gidansa da ke nan Fatima Shema Estate."

Marigayi Nasir ne mashawarci na musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari kan Kimiyya da Fasaha kafin a nada shi Kwamishina.

Amma da Daily Trust ta ziyarci gidansa, wani mutum, da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun daren jiya aka kashe shi.

Ya ce:

"An daba masa wuta ne a cikinsa a yayin da ya ke zaune a falonsa sannan aka ja gawarsa zuwa bandaki aka rufe."

An haife shi ne a garin Mani da ke karamar hukumar Mani na jihar Katsina.

Ku dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel