Edo: Ɗalibai sun yi wa ɗan sanda tumɓur, shugaban makaranta ya tsere bayan sun ƙone makaranta

Edo: Ɗalibai sun yi wa ɗan sanda tumɓur, shugaban makaranta ya tsere bayan sun ƙone makaranta

  • Daliban makarantar sakandare a jihar Edo sun yi wa dan sanda tsirara, sun kone wani bangare na makarantarsu sannan sun fatattaki malamai da shugaban makaranta
  • Kamar yadda wata majiya ta sanar, an tura 'yan sandan ne domin tsaro yayin da daliban ke jarabawa amma kwatsam suka dinga jifan 'yan sandan da dutse da makamai
  • 'Yan sandan jihar sun kasa komai har sai da jami'an DSS suka bayyana tare da fara harbi, daliban sun watse kafin daga bisani aka damke arba'in da tara daga ciki

Edo -'Yan sanda sun damke kusan dalibai 49 na makarantar sakandaren Idogbo da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha ta jihar Edo kan zarginsu da ake yi da kone wani bangaren makarantar tare da tarwatsa ofishin shugaban makarantar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, Bello Kontongs, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata tattaunawa da yayi da Punch a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

Edo: Ɗalibai sun yi wa ɗan sanda tumɓur, shugaban makaranta ya tsere bayan sun ƙone makaranta
Edo: Ɗalibai sun yi wa ɗan sanda tumɓur, shugaban makaranta ya tsere bayan sun ƙone makaranta. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da ta gabata. A wani bidiyo da ya bazu na lamarin a ranar Talata, an ga daliban na bin wani mutum wanda aka gano cewa shugaban makarantar ne.

A yayin da suka kasa kama shi, daliban sun koma farfajiyar makarantar inda suka dire da fushinsu kan kayan gwamnati, Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa daliban sun balle rashin mutuncinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda da aka tura makarantar domin kwantar da tarzomar, suka fi karfin wani dan sanda kuma suka masa tsirara.

Wata majiya daga makarantar wacce ta bukaci a boye sunanta, ta ce hukumar makarantar ta gayyaci jami'an tsaron domin magance duk wani rashin tsaro da ka iya tasowa ballantana a wannan lokacin na shagulgula da jarabawa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fattataki 'yan bindiga, sun ceto wani matashi dan shekara 17 a Kaduna

Majiyar ta kara da cewa, "Ya zama al'ada a kowanne karshen zangon karatu, muna gayyatar jami'an tsaro domin gujewa karya doka. Za a kammala jarabawa kuma za a yi hutu.
"Amma kwanaki kadan kafin jarabawar, mun fara gwagwarmaya da dalibai kan yadda suke wurga abubuwa masu fashewa a farfajiyar makarantar.
"A lokacin da aka fara jarabawar a ranar Juma'a 3 ga Disamba, mun gayyaci 'yan sanda da 'yan sintiri. Daya daga cikin 'yan sandan na tsaka da sintiri sai kawai muka ga dalibai sun biyo shi. Abokan aikinsa sun je ceton shi amma dalibai na jifansu da dutse da makamai.
"A lokacin da aka kasa shawo kansu, malamai sun fara tserewa yayin da daliban suka fara barna kuma an kasa shawo kan lamarin.
“Mun gayyaci jami'an tsaro na farin kaya wadanda suka yi amfani da harbin bindiga domin tsorata su. Daga bisani ne DSS suka kama dalibai arba'in da biyar wadanda suka boye a daji. Yanzu haka suna hannun 'yan sanda."

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Kontongs ya ce, "Dalibai arba'in da tara na hannunmu kan barnata kayan gwamnati da suka yi. Babu wanda muka kai kotu har yanzu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel