Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

  • Jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas, Karibi Bob Manuel, ya ce bai ga alamar cewa matasan kasar nan sun shirya karbar mulki ba
  • Dan siyasan ya sanar da cewa har yanzu matasan bibiyar tsofaffin suke yi kuma babu alamun alkibla ko tunanin karbar shugabanci
  • Ya shawarcin matasan Najeriya da su tashi tsaye tare da shirya kansu a jam'iyyun siyasa ta yadda za su yi tsofaffi ritayar dole

Mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas, Karibi Bob Manuel, ya ca matasan Najeriya ba su da ra'ayin bibiyar shugabanninsu domin karbar shugabanci.

BobmManuel ya sanar da kamfanin daillancin labaran Najeriya a Fatakwal jihar Ribas a ranar Juma'a cewa, yanayin yadda matasa ke martani kan manyan abubuwan da ke faruwa a kasar nan ne ya nuna hakan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC
Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Muna cikin wani hali wanda matasa suke nuna kamar komai daidai tare da sakarcin bibiyar shugabannin siyasa ba tare da wani tunani ba.
"Matasa suna yi kamar wasu wadanda aka siya ko kuma marasa alkibla wadanda a koyaushe ake juya mu son rai tamkar sakako kuma ake nuna mana abinda ya dace mu yi," ya jajanta.

Kamar yadda Bob Manuel yace, a yanzu bai kai shekaru biyu ba zuwa zaben 2023 ba, matasa ba su shirya ba kuma ba su kimtsa tunkarar tsofaffin nan da ke rike da madafun iko ba, Daily Trust ta ruwaito.

"Za a fara shirin zabe a shekarar 2022 amma matasa har a halin yanzu ba su shirya ba kuma basu da inda suka dosa.
“Har sai mun shirya kanmu, mun hada kai tare da yin magana da murya daya, komai rabuwar kansu a siyasance, tsofaffin za su cigaba da shugabantar mu," yace.

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

Jigon jam'iyyar APC ya yi kira ga matasan Najeriya da su cigaba da rijistar katin zabe domin su iya juya akwatunan zabensu yadda suka so.

"Kada mu kuskura mu nuna ba mu damu da gaba ba, mu tabbatar da cewa mun saka 'yan Najeriya sun yi rijista tare da samun katin zabe kafin 2023.
"Idan muka shirya kanmu a jam'iyyun siyasa daban-daban, za mu iya hada kai tare da hana wadannan tsofaffin cigaba da mulkar mu," Bob Manuel yace.

Anambra: Jam'iyyun siyasa 11 ne suka maka Soludo a kotun karar zabe

A wani labari na daban, jam'iyyun siyasa tare da 'yan takara sun mika korafi inda suke kalubalantar nasarar dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, Farfesa Charles Soludo a zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra.

Masu korafin sun yi gaggawar mika korafin kafin cika kwana 21 bayan zaben kamar yadda sakataren kotun sauraron kararrakin zabe, Surajo Gusau ya sanar.

Kara karanta wannan

Ayu Iyorchia: APC ita ce gagarumar cutar 'kansar' da ta addabi Najeriya

Vanguard ta ruwaito cewa, ya ce jam'iyyun sun mika korafe-korafensu ne tsakanin Litinin zuwa Talata, a lokacin da ba a yi tsammanin cewa akwai 'yan takarar da aka lallasa ba da zasu kalubalanci nasarar Soludo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel