Alkalin Katsina na hannun 'yan bindiga bayan kwana 27 da sace shi, iyalansa sun koka

Alkalin Katsina na hannun 'yan bindiga bayan kwana 27 da sace shi, iyalansa sun koka

  • Shehu Yakubu alkalin kotun shari'a ne na karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina wanda 'yan bindiga suka sace
  • Har bayan sace alkalin da kwanaki 27, babu amo balle labari duk da iyalansa sun tabbatar da cewa sun samu wasika 2 daga miyagun
  • 'Yan bindigan sun bukaci kudin fansa har N15 miliyan amma sun kone motar alkalin a titi kafin su tasa keyarsa zuwa daji

Katsina - Iyalan alkalin kotun shari'a ta jihar Katsina, Shehu Yakubu, sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ceto alkalin wanda aka yi garkuwa da shi tun kwanaki 27 da suka gabata, Premium Times ta ruwaito.

Yakubu, wanda shi ne alkalin kotun shari'a da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar, an sace shi tare da kanwar matarsa a watan da ya gabata yayin da ya ke komawa Funtua bayan kammala aikinsa.

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

Alkalin Katsina na hannun 'yan bindiga bayan kwana 27 da sace shi, iyalansa sun koka
Alkalin Katsina na hannun 'yan bindiga bayan kwana 27 da sace shi, iyalansa sun koka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, daya daga cikin 'ya'yansa, Mustapha Shehu ya sanar, ya ce 'yan bindigan sun kone motar alkalin kirar Peugeot 406 kafin su yi awon gaba da shi.

Iyalan sun ce 'yan bindigan sun tuntube su sau biyu bayan sace shi amma ba su sake ji daga wurinsu ba bayan nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sau biyu suna rubuto mana wasika inda suke bukatar kudi har N15 miliyan amma ba mu da kudin. Kuma datse kafofin sadarwa a yankin yasa ba mu cigaba da ciniki ba. Tun daga nan ba mu sake ji daga wurin su ba," Shehu yace.

Kamar yadda yace, 'yan bindiga ba su sake tuntubarsu ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isa, bai daga wayarsa ba kuma bai yi martani kan sakon kar ta kwana da aka tura masa.

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

Rundunar 'yan sanda ta sanar da yadda miyagu suka yi garkuwa da DPO a Edo

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Edo ta tabbatar da garkuwa da DPO, CSP Ibrahim Ishaq na ofishin yankin Fugar da ke karamar hukumar Etsako ta jihar da miyagun 'yan bindiga suka yi.

A wata takarda, kakakin rundunar, Bello Kongtons, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Philip Ogbadu, ya ce an sace DPO a ranar 26 ga watan Nuwamban 2021.

"DPO na kan hanyarsa ta zuwa Aghenebode a motarsa tare da dogarinsa Sajan Aliyu kuma duk suna sanye da farin kaya ne yayin da miyagun suka tsare su a wurin Ekwuosor," takardar tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel