Kamfanonin man Duniya sun tattara kudinsu, su na barin Najeriya zuwa wasu kasashen Afrika

Kamfanonin man Duniya sun tattara kudinsu, su na barin Najeriya zuwa wasu kasashen Afrika

  • Najeriya ta rasa matsayinta na kasar ta da fi kowacce hako danyen mai a duk fadin nahiyar Afrika
  • Baya ga haka, Najeriya na fuskantar takara a kasuwa wajen Libya da yanzu ta sha gaban kowa
  • Wasu kamfanonin kasashen ketare sun bar Najeriya a yanzu, sun zabi su koma Arewacin Afrika

Nigeria - An doke Najeriya a matsayinta na kasar Afrikar da ta zarce sa’a wajen hako danyen mai. Lamarin ya canza a wannan shekara ta 2020.

A daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ba ta gama jimamin wannan rashi ba, sai kuma aka ji cewa kamfanonin mai su na gujewa Najeriyar

Jaridar BusinessDay ta fitar da rahoto cewa kamfanoni irinsu TotalEnergies SE da Eni SpA na kasar Italiya su na shirin komawa kasar Libya.

Kara karanta wannan

Shirin kidaya yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa

Wadannan kamfanoni za su narka Dala biliyan biyu a aikin man da kamfanin Waha Oil yake yi, domin adadin man da kasar take haka ya karu.

Yadda Libya za ta amfana

Rahoton yace kamfanonin su na sa ran su kara yawan danyen man da kamfanin Waha Oil yake hakowa a kullum ya karu da ganguna 100, 000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan kudi da kamfanonin za su narka zai taimaka sosai wajen hako mai a rijiyar Mabruk.

Kamfanonin man Duniya
Alkaluman hako mai Hoto: Facebook / OPEC
Asali: Facebook

Baya ga arzikin mai da Libya za ta samu, wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen samar da megawatts 500 na karfin wuta daga hasken rana.

Libya ta sha gaban Najeriya

Libya ta sha gaban kowace kasar Afrika a arzikin mai. Ana hasashen cewa ta na da ganguna biliyan 43 na arzikin mai da kubic mita miliyan daya na gas.

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

Matsalar tsaro ce ta hana Libya kai intaha wajen hako danyen mai da gas a ‘yan shekarun nan. Amma yanzu ana sa ran yakin basasa ya zo karshe.

Legit.ng tace ana tunanin kamfanonin ketaren su na ficewa daga Najeriya ne saboda matsalar tsaro. Ana kukan yawan bumburutu da fasa bututun mai.

Za a rika ba talakawa N5, 000 a 2022

Ministar tattalin arziki da kasafin kudin Najeriya, Zainab Ahmed tace kwamitin da yake aiki a kan yadda za a rage radadin cire tallafin fetur yana ta aiki.

Ahmed tayi bayanin yadda za a rabawa talakawa N5, 000 idan fetur ya kara tsada, tace za so a ce sun yi abin da ya wuce wannan, amma babu isassun kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel