Hotunan gidaje 10 mafi kyau da tsada a Najeriya
Najeriya ta kasanace gidan wasu mashahuran manyan masu kudi a Afirka. Daga cikin mashahuran masu kudin sun hada da ‘yan kasuwa da masu nishadantarwa. Saboda yanayin halin da kasar ke ciki, ba kasafai ake ganin gine-gine na alfarma ba. A wannan rubutun akwai hotuna tare da darajar wasu katafaren gidaje a kasar nan.
Katafaren gidan Folorunsho Alakija
Gidan ya kai darajar dala miliyan dari bakwai. Ba wai a Najeriya ya fi kowanne gida tsada ba, shine gida mafi tsada da mace ta mallaka a duniya kuma na hudu mafi tsada a fadin duniya.
Gidan Mike Adenuga
Gidan na nan a Banana Island da ke Legas. Yana da darajar naira biliyan takwas. Arzikin Mike Adenuga ya dogara ne da man fetur, iskar gas da kasuwanci a fannin sadarwa.
Katafaren gidan Aliko Dangote
Mashahurin dan kasuwar ya yi shekaru biyar kenan da gina gidansa da ke Abuja. Gidan ya kai darajar naira biliyan biyar.
Gidan P-Square
Peter da Paul dai sanannun mawaka ne masu matukar nishadantarwa a Najeriya. Sun gina katafaren gidan ne a Banana Island da ke Legas. Darajar gidan ya kai naira biliyan 1.5.
Katafaren gidan Sanata Dino Melaye
Sanatan ya yi suna a Najeriya ne ta kasaitattun motocin alfarma da ya mallaka. Son hutawarsa bai tsaya a nan ba, ya gina gida na kimanin naira biliayn 1.5.
Katafaren gidan Bola Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma jigo a jam’iayyar APC. Yafi kowanne dan siyasa arziki a Najeriya. Katafaren gidanshi da ke titin Bourdillon da ke Ikoyi ya kai darajar naira biliyan daya.
Gidan Sanata Lee Maeba
Shine sanata mafi karancin shekaru a Najeriya. Sanatan ya mallaki gidansa ne a garin Fatakwal mai darajar naira biliyan daya.
Katafaren gidan Linda Ikeji
Gidan marubuciyar na nan a Banana Island kuma ya kai darajar naiar miliyan 600.
Gidan E-Money
Emeka okonkwo babban dan kasuwa ne. Ya mallaki gida mai darajar naira miliyan 250 a tsibirin Legas.
Sansanin Neya
Sansanin Neya Mallakin tsohon Gwamnan jihar Abia ne, Orji Uzor kalu. Duk da ba a san darajar wannan gida ba, amma ana hasahen ya kai biliyoyin nairori.
DUBA WANNAN: Zamfara: Kotu ta tsare tsohon kwamishinan Yari da aka gurfanar da laifin satar Shanu da garkuwa da mutane
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng