'Yan gudun hijira na bukatar gidaje yayin da gwamnati za ta rufe sansanoninsu a Borno

'Yan gudun hijira na bukatar gidaje yayin da gwamnati za ta rufe sansanoninsu a Borno

  • Mazauna sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno suna ta murnar rufe sansanoninsu da gwamnatin jihar za ta yi a cikin kwanakin nan
  • Amma kuma ba nan gizo ke sakar ba, sun bayyana damuwarsu balle a kan 'ya'yansu da ke karatu a makarantun gaba da sakandare da za su bari a yankin
  • Shugaban mata 'yan gudun hijira da ke sansanin Bakassi, ta jinjina wa Gwamna Zulum kan kokarinsa kuma ta ce hakan na nuna daawwamar tsaro

Borno - Da yawa daga cikin 'yan gudun hijaran da ke sansanin Bakasssi sun bayyana son komawarsu gida tare da komawa ayyukan nomansu domin samun rufin asiri a maimakon dogaro da tallafi.

Sai dai, sun bayyana damuwarsu kan makomar 'ya'yansu wadanda ke karatu a makarantun gaba da sakandare ba tare da wurin kwana ba, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Gwamnatin jihar Borno a cikin kwanakin nan ta bayyana shirin ta na rufe dukkan sansanonin 'yan gudun hijira bayan dawowar zaman lafiya a yankunan da 'yan Boko Haram suke.

'Yan gudun hijira na bukatar gidaje yayin da gwamnati za ta rufe sansanoninsu a Borno
'Yan gudun hijira na bukatar gidaje yayin da gwamnati za ta rufe sansanoninsu a Borno. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Asabar, Gwamnan jihar Babagana Zulum ya ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira da ke Bakasssi inda ya sanar da mazauna wurin cewa za a rufe shi kuma za a basu dukkan taimakon da ya dace.

A watan Mayun da ta gabata ne gwamnatin ta rufe sansanin 'yan gudun hijira da aka kafa a kwalejin Mohammed Goni inda aka koma karatu, Daily Trust ta wallafa.

Masu gudun hijira daga kananan hukumomin Marte, Gwoza, Monguno da Guzamala suna rayuwa a sansanin Bakasssi na shekaru bakwai saboda ta'addanci. Da yawansu sun bar gidajensu bayan 'yan ta'addan sun tarwatsa su.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

Shugaban mata 'yan gudun hijira ta karamar hukumar Gwoza da ke sansanin Bakassi, Hauwa Amadu, ta yi maraba da hukuncin gwamnatin jihar na taimakon 'yan gudun hijira su koma gidajensu.

Ta ce da yawa daga cikin iyalan da suka yi gudun hijirar suna rayuwa ne sansanonin saboda basu da yadda za su yi kuma duk wani yunkurin mayar da su gida zai tabbatar da sun samu dogaron kansu ne.

"Ba mu da yadda za mu yi ne, amma zamanmu a sansanin na shekaru 7 saboda kauyukan duk sun lalace ne sakamakon ta'addanci," yace.

Ta ce baya ga Gwoza, Pulka, Izge da wasu tsirarun garuruwa, da yawa daga cikin kauyukan Gwoza babu mutane, wanda hakan ne yasa jama'a daga Amagda, Guduf, Kuranabasa, Wala, Dure da Gasha suke rayuwa a wasu wuararen.

Ta ce shirin gwamnatin jihar na aike wasu 'yan gudun hijira daga karamar hukumar Gwoza zuwa Maiduguri da Limankara hanya ce ta samar musu isasshen wurin zama da tsaro.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri

A wani labari na daban, wata mummunar gobara ta yi ajalin wani jariri a wani sansanin 'yan gudun hijira dake wuraren titin Mafa a cikin Maiduguri jihar Borno a ranar Talata.

Ganau sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da misalin 7:30am na safiya a wani bangare na sansanin amma an samu nasarar kashe gobarar cikin karamin lokaci.

A cewar ganau din: "Wata gobara ta barke da misalin 1pm kuma ta yi sanadiyyar kone tanti da dama dake sansanin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel