Basaraken Katsina da wani dalibi sun samu yanci bayan kwanaki 26 a hannun masu garkuwa da mutane

Basaraken Katsina da wani dalibi sun samu yanci bayan kwanaki 26 a hannun masu garkuwa da mutane

  • Masu garkuwa da mutane sun saki Maigarin Banye da ke jihar Katsina, Bashir Gide tare da wani dalibin sakandare da suka sace
  • Basaraken da dalibin sun samu yanci ne bayan sun shafe kwanaki 26 a hannun wadanda suka yi garkuwa da su
  • Wani dan uwan basaraken da ya tabbatar da sakin na su ya ce an biya kudin fansa kafin aka sako su a yammacin yau Laraba, 10 ga watan Nuwamba

Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun saki Bashir Gide, Maigarin Banye a karamar hukumar Charanci da ke jihar Katsina da kuma wani dalibi bayan kwanaki 26 da yin garkuwa da su.

An saki basaraken a yammacin ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, da dalibin makarantar sakandare wanda aka sace su tare a watan Oktoba.

Basaraken Katsina da wani dalibi sun samu yanci bayan kwanaki 26 a hannun masu garkuwa da mutane
Basaraken Katsina da wani dalibi sun samu yanci bayan kwanaki 26 a hannun masu garkuwa da mutane Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Maigari Gide yana da nasaba da Bala Almu Banye, wani kwamishinan tarayya a hukumar kidaya ta kasa.

Read also

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Wani dan uwan basaraken, Nura Banye, ya tabbatar da sakin nasa a yammacin yau Laraba, amma ya ce bai san nawa aka biya masu garkuwan ba a matsayin kudin fansa, rahoton Premium Times.

Ya ce:

"Na yi magana da yan uwana a garin kuma sun tabbatar mani da cewa yana gida sannan kuma an biya kudin fansa kafin sakin nasa a yammacin nan. An kuma biya kudin fansar dayan yaron da aka sace tare da basaraken."

Ya ce tuni Gide ya sadu da iyalansa.

Rahoton ya kuma kawo cewa kakakin yan sandan jihar, Gambo Isa, ya ce bai da labarin sakin basaraken a yammacin nan.

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

Read also

Na sha banban da sauran yan siyasa, ni ba makaryaci bane – Mataimakin gwamnan Edo

A wani labarin kuma, mun ji cewa akalla mutane 15 ciki harda matan aure uku ne suka rasa ransu a kauyukan Binnari da Jab Jab a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Binnari da misalin karfe 4:00 na asuba a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, inda suka dunga harbi kan mai uwa da wabi.

An tattaro cewa mutanen kauyukan sun yi yunkurin yakar su amma sai yan bindigar wadanda yawansu ya fi 50 suka sha karfinsu.

Source: Legit.ng

Online view pixel