Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci

Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci

  • Shugaba Buhari ya zanna da manyan yan kasuwa a ziyarar aikiin da ya ke a kasar Faransa
  • Wannan ya biyo bayan jawabin da yayi ranar Laraba na kira ga attajiran kasashen waje su zuba hannun jari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kamfanin man Total Mr Patrick Pouyanne tare da tawagar diraktocinsa a ranar Alhamis, 11 ga Nuwamba, 2021.

Buhari ya karbi bakuncinsu ne a masaukinsa a Paris, babban birnin kasar Faransa, mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya bayyana.

Daga cikin tawagar yan kasuwa akwai Shugaban Total na kasar, Mike Sangster; SVP Africa EP Total Energies Henri-Mike Ndong-Nzue, da shugaban E&P TOTAL Energies Nicolas Terraz.

Jami'in gwamnatin Najeriya da suka halarci ganawar sune Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari; Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; da Shugaban hukumar NAPIMS, Bala Wunti.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aikawa takwararsa na Nijar sakon ta'aziyya bisa gobarar da tayi ajalin dalibai 25

Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total
Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya gana da Shugaban Bankin Cigaba na Musulunci

Hakazalika Shugaba Buhari ya gana da Shugaban bankin cigaban Musulunci Dr. Muuhammad Suleiman Al-Jasser.

Bayan haka kuma ya gana da shugaban PEA Salah Mansour da ISDB SRC Assane BA

Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci
Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci
Shugaba Buhari ya gana da manyan diraktocin Kamfanin Total da Shugaban bankin Musulinci
Asali: Facebook

Na zuba makudan kudi don farfado da tattalin arziki da inganta rayukan yan Najeriya: Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta farfado da tattalin arzikin Najeriya, ya gina manyan ayyuka da kuma inganta jindadin yan Najeriiya.

Buhari ya bayyana hakan ne ga masu zuba hannun jari a kasar Faransa ranar Laraba yayin taron hadin kai tsakanin Najeriya da yan kasashen waje.

Shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta zuba makudan kudi wajen ilmantar da mutane, kara ingancin asibitoci, manya ayyuka, karfafa mata yakar sauyin yanayi da samar da abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel