Tana matukar bani sha'awa duk da sa'ar kakata ce, Cewar Saurayin da auri 'yar shekara 61

Tana matukar bani sha'awa duk da sa'ar kakata ce, Cewar Saurayin da auri 'yar shekara 61

  • Wani dan shekara 24 mai suna Quram ya auri masoyiyarsa Cheryl bayan shekaru takwas suna tare
  • Sabuwar amaryar yar shekara 61 ce kuma tana da 'yaya takwas, amma duk da haka Quram yace yana matukar son ta
  • Ya bayyana yadda suke soyewa kullu yaumin kuma tana matukar bashi sha'awa

Soyayya akace makauniya ce kuma hakan ya bayyana karara a labarin soyayyar dan shekara 21 Quram da sabuwar Amaryarsa yar shekara 61 Cheryl.

Tun lokacin da labarin aurensu ya yadu a kafafen sada zumunta, mutane na tofa albarkatun bakinsu kuma masoyan sun bayyana yadda suke matukan son juna.

Tana matukar bani sha'awa duk da sa'ar kakata ce
Tana matukar bani sha'awa duk da sa'ar kakata ce, Cewar Saurayin da auri 'yar shekara 61 Hoto: Screengrabs from video shared by Love Don't Judge
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

Ta yaya suka hadu?

A Intabiyun da shafin Love Don't Judge a Facebook ya watsa, masoyan an ga hotunan masoyan suna sumbatar juna saboda soyayya.

A cewarsa, sun hadu ne a shafin Tiktok kuma kawai sai suka fara son juna.

Matashin yace shine ya fara fadawa Cheryl yana sonta kuma ta yarda.

Ya bayyana cewa mutane da dama suna sukarsa cewa matar ta girme sa kuma ya auri sa'ar kakarsa, yayinda wasu kuma suka ce kawai kudi yabi.

Amma ko a jikinsu

Ya kara da cewa bai damu da maganganun jama'a ba kuma iyayensa sun amince da auren.

Ita kuwa Cheryl tace 'yaya 8 gareta kuma basu tare da ita.

Source: Legit.ng

Online view pixel