Masu garkuwa sun sa kudi da miyagun kwayoyi a matsayin fansar mutanen da suka dauke

Masu garkuwa sun sa kudi da miyagun kwayoyi a matsayin fansar mutanen da suka dauke

  • ‘Yan bindiga sun sace wasu mutane da suka kai hari a karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun.
  • Miyagun sun bukaci a biya Naira miliyan 10 da miyagun kwayoyi domin a fanshi wadanda aka sace.
  • Mutanen gari sun ce an tuntube su, an bukaci su kawo Naira miliyan 10, codeine, tabar wiwi, da abinci.

Ogun - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace mutane uku a jihar Ogun, a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2021.

Jaridar Punch tace ‘yan bindigan sun bukaci a kawo abinci, Naira miliyan 10 da miyagun kwayoyi a matsayin fansar wadannan mutanen da suka dauke.

‘Yan bindigan sun kuma harbe mutum daya wanda ya yi yunkurin ya tsere bayan sun damke shi.

Rahoton yace ‘yan bindigan sun boye ne a cikin dajin Obada-Oko, karamar hukumar Ewekoro, jihar Ogun, suka rika addabar mutanen yankin Ewekoro.

Read also

Paris Club: Minista, Gwamnoni na rigima kan biliyoyin da aka biya masana daga asusunsu

Daily Post tace miyagun ‘yan bindigan sun dauke mutane ukun bayan an yi ba-ta-kashi tsakaninsu da dakarun ’yan sandan reshen Obada-Oko, Ogun.

Gwamnan Ogun
Gwamna Dapo Abiodun Hoto: guardian.ng
Source: UGC

‘Yan bindiga suna fake a Ogba Kehinde

Wani wanda ya sha da kyar a hannun ‘yan bindigan, Razak Lasisi, ya shaidawa manema labarai yadda abin ya wakana da aka tuntube shi a wayar salula.

Mista Razak Lasisi yace lamarin ya auku ne a ranar Asabar, a lokacin da yake kokarin dawowa gida bayan ya tashi aiki da kimanin karfe 9:00 na dare.

Lasisi wanda tsohon shugaban makarantar sakandare ne, yace wadannan ‘yan bindiga sun yi kokarin sace shi a wani wuri da ake kira Ogba Kehinde.

An bukaci 'yanuwa da abokai su biya fansa

A cewar Lasisi, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi jama’a, sun ce su biya kudin fansar wadanda suka dauke, sun bukaci a kawo masu kwayoyi.

Read also

'Yan bindiga sun bude wa wasu fasinjoji wuta sun halaka 3, sun kuma ƙona babura 10

“Sun ce a biya Naira miliyan 10, kuma a hada da codeine, tabar wiwi, ruwa da kayan abinci.” - Razak Lasisi.
“Amma bayan an yi ta rokonsu, sun rage kudin fansar zuwa N1.5m, da codein, ruwa da kayan abinci.”

Rashin tsaro a Arewa

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya tunawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa zai yi bayani a kan batun rashin tsaro.

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yace ana yawan kashe mutane a Arewa, yace mutane sun samu amfanin noma, amma ba a isa a shiga gona a dauko amfanin ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel