Maigida ya kori mai haya daga gidansa saboda yawan kawo mata gida da yakeyi

Maigida ya kori mai haya daga gidansa saboda yawan kawo mata gida da yakeyi

  • Wani mai gida ya baiwa mai hayan daki a gidansa takardar notice kan yawan kawo yan mata gidan
  • A cewar mai gidan, gaskiya lalacin da mutumin ke yi ya ishe sa kuma an gargadesa amma ya ki ji
  • Mutane da dama a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu

Wani mai gida ya yi kira ga mai haya a gidansa ya shirya tattara inasa-inasa ya bar masa gida idan kudinsa ya kare saboda yawan kawo yan mata marasa aure gidan.

A takardar da ta yadu a kafafen sada zumunta ta shafin Gist Ville, mai gidan ya ce mai hayan ya saba kawo mata iri-iri gidan kullum.

A wasikar da maigidan ya turawa mai hayan mai suna Babajide, ya bayyana cewa dalilin da yasa ya yanke shawaran shine ya gargadesa sau da dama amma bai ji ba.

Read also

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

Yanzu mai gidan ya bashi nan zuwa karshen watan Nuwamba 2021 ya bar masa gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maigidan ya kori mai haya daga gidansa saboda yawan kawo mata gida da yakeyi
Maigidan ya kori mai haya daga gidansa saboda yawan kawo mata gida da yakeyi Photo Credit: Kola Sulaimon, Facebook/Gist Ville
Source: Getty Images

Me wasikar ta kunsa

Wasikar mai kwanar wata, 27 ga Satumba, 2021, mai gidan yace:

"Kudin hayanka zai kare 30 ga Nuwamba, 2021 kuma bana son ka sake biya. Ba zan cigaba da lamuntan Zinace-zinacenka na kawo mata iri-iri cikin gidan nan ba."
"Mun dade da gargadinka ka daina wannan lalatan amma ka ki ji."
"An baka nan da karshen Nuwamba ka bar gidan da kake zama yanzu."

Source: Legit.ng

Online view pixel