Gaskiya ta fito: Yadda aka yaudari ‘Yan Najeriya a kan batun digirin Dino Melaye a Jami’ar Baze

Gaskiya ta fito: Yadda aka yaudari ‘Yan Najeriya a kan batun digirin Dino Melaye a Jami’ar Baze

  • Sanata Dino Melaye ya karanta ilmin shari’ar a Jami’ar Baze da ke Abuja
  • Ana ta yawo da labari cewa har Melaye ya zama gwarzon daliban shekara
  • Binciken kwa-kwaf da aka gudanar, ya nuna ba gaskiyar batun ba kenan

Abuja - A karshen makon jiya ne aka yi ta yamadidi da wani labari cewa Sanata Dino Melaye ya kammala karatu a jami’a a matsayin gwarzon shekara.

Jita-jitar tace Dino Melaye ya karanta ilmin shari’a, kuma shi ne ya zama haziki a kaf ajinsu. Jaridar Premium Times ta yi bincike a kan wannan batu.

Babu shakka Sanata Ifeanyi Ubah, Osita Chidoka da Dino Melaye sun yi karatun digiri a jami’ar Baze da ke Abuja, amma an yi wa labarin karin gishiri.

Kara karanta wannan

Wike ya yi kaca-kaca da mulkin Buhari, yace abubuwa ba su taba tabarbarewa haka ba

An fara ganin wannan labari ne a shafin Dorathy Bachor Lovers a Facebook, bayan Baze ta yaye dalibanta, inda aka ce Dino Melaye ne ya yi fice a ajinsu.

‘Yan jarida sun yi ta daukar wannan labari, har ana bata sunan jami’ar. Wani rahoton yace mafi yawan lokutan da ake karatu, Melaye yana kasashen waje.

Dino Melaye a Jami’ar Baze
Dino Melaye ya gama makaranta Hoto: www.hotnaija.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Melaye, Ubah, Chidoka sun koma makaranta, amma ...

Dubawa wanda ke kokarin bibiyar gaskiyar labarai, ta tuntubi magatakardar jami’ar Baze, Mani Ahmad, wanda ya yi karin haske a kan abin da ya wakana.

Takardun da aka samu na bikin yaye daliban jami’ar sun nuna cewa lallai Dino Melaye ya samu shaidar digiri, amma sam bai zama gwarzon shekara ba.

A takaita bayani dai, tsohon Sanata na jihar Kogi bai ma gama jami’ar da matakin farko na Digiri ba.

Kara karanta wannan

Dalibin Najeriya ya kammala digiri bayan shekaru 13 ana gwagwarmaya a Jami'ar UNIJOS

Rosemary Keccy Busari ce ta ciri tuta ba Dino Melaye ba

Kamar yadda Reuben Abati ta kawo rahoto, abin da yake tabbas shi ne wata Baiwar Allah mai suna Rosemary Keccy Busari ce ta ciri tuta ba Melaye ba.

Miss Rosemary Keccy Busari ce ta zama gwarzon daliban ilmin shari’a a jami’ar Baze. Dalibar ta gama digiri ne da matakin farko da ake kira ‘First Class’.

Kyari-Hushpuppi: Dino ya wanke kansa

Kwanakin baya Sanata Dino Melaye ya karyata zargin da ake yi masa na karbar wani kason kudi daga hannun shahararren 'dan damfarar nan, Hushpuppi.

Melaye yace babu wani dalili da yake nuna Hushpuppi ya taimaka masa wajen sace wasu kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel