Kyari-Hushpuppi: An zargi Dino Melaye da karbar na shi rabon $31m, ya karyata

Kyari-Hushpuppi: An zargi Dino Melaye da karbar na shi rabon $31m, ya karyata

  • Sanata Dino Melaye ya karyata zargin da ake masa na karbar nashi rabon daga hannun Hushpuppi
  • A cewarsa, babu wani dalili da yake nuna Hushpuppi ya taimaka masa wajen sace wasu kudade
  • Ya kuma kalubalanci masu yada jita-jitar cewa, idan akwai su kawo shi kadan daga ciki yake bukata

Abuja - Wani tsohon sanata a Najeriya, Dino Melaye, ya yi magana a kan rahotannin da ke ci gaba da alakanta shi da wani dan damfara, Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Melaye a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Instagram a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ya ce rahotannin kafofin sada zumunta na nuna cewa Hushpuppi ya taimaka masa wajen satar dala miliyan 31, a cewarsa batu ne na karya.

Ya ce idan rahoton gaskiya ne, zai bukaci dala miliyan 1 daga cikin kudaden da ake zargin an sace, yana mai cewa wadanda suka fara yada jita-jitar za su iya rike sauran dala miliyan 30.

Kara karanta wannan

Tsohon sanatan Najeriya ya mayar da martani bayan hotonsa ya sake bayyana tare da dan damfara, Hushpuppi

Kyari-Hushpuppi: An zargi Dino Melaye da karbar na shi rabon $31m, ya karyata
Sanata Dino Melaye | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: Depositphotos

Yace:

"Na karanta yanzu a Twitter da Instagram cewa Hushpuppi ya taimaka wa Dino Melaye ya saci dala miliyan 31.
“Don Allah daga cikin wannan dala miliyan 31, na baku dala miliyan 30. Ku bani dala miliyan daya kawai. Ya ishe ni. Wannan muryar fatalwar $31m da Huspuppi ya taimaka na sata. Domin sun ce FBI ta Amurka ta kame ni. Bayan watanni biyu da nayi a Amurka, watakila sun manta su kama ni a filin jirgin sama.''

Daya daga cikin mabiyan Melaye yayi tsokaci akan bidiyon.

Tosin Marie ta rubuta:

"Dole ne ku amsa duk zargin da ake yi maka?? ''

Ban damu da yada hoto na da Hushpuppi

A baya Melaye ya ce bai damu da yadda hotonsa ke yawo da Hushpuppi ba.

Melaye a cikin wata sanarwa ta shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi kira ga jama’a da su daina watsa hotunansa da fitaccen dan damfaran.

Kara karanta wannan

Ya dasa sabon zargi: Abba Kyari ya goge wallafar da yayi a shafinsa inda yayi bayanin alakarsa da Huspuppi

Yace:

"Babu lokacin da zan nemi mutane da kada su sanya hotunana tare da Hushpuppi ko wani don wannan lamarin saboda babu wani dalili."

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

A wani labarin daban, Hadin gwiwar Kungiyoyin Arewa sun yi zargin cewa cibiyar bincike ta FBI da rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) sun take hakkin Abba Kyari kai tsaye na bincikensa da ake.

A cewar kungiyar, Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP), ba a ba shi damar yin bayani ba kawai FBI da NPF suka dauki matakin gaggawa a kansa.

Don haka, sun nemi a gaggauta duba dakatarwar Kyari sannan a mika shari'arsa ga Hukumar Leken Asiri ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel