Mai zai iya kara tsada, Gwamnati za ta daina biyan tallafin fetur a tsakiyar shekara mai zuwa

Mai zai iya kara tsada, Gwamnati za ta daina biyan tallafin fetur a tsakiyar shekara mai zuwa

  • Gwamnatin Tarayya za ta daina biyan tallafin man fetur nan da shekarar 2022
  • Ministar kudi, Zainab Ahmed ce ta bayyana wannan a wajen wani taro a Abuja
  • Babban bankin Duniya tace tallafin zai ci wa Najeriya N2.9tr a shekarar bana

Abuja - Babban bankin Duniya ya koka game da yadda gwamnatin Najeriya ta ke batar da makudan kudi wajen biyan tallafin man fetur a kasar nan.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnatin Muhammadu Buhari za ta kashe har Naira Tiriliyan 2.9 a bana da sunan tallafin fetur domin a iya saida mai da araha.

Jiya darektan babban bankin Duniya a Najeriya, Shubham Chaudhuri ya yi magana a wajen taron tattalin arziki na kasa wanda ake shiryawa a garin Abuja.

Read also

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

Da yake jawabi a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, 2021, Shubham Chaudhuri yace kason tallafin fetur ya zarce na kiwon lafiya, ilmi da samar da tituna a 2021.

Shubham Chaudhuri ya koka da tsarin Najeriya

“A shekarar nan, Najeriya na kan hanyar kashe Naira tiriliyan 2.9 a tallafin man fetur, wanda hakan ya zarce abin da ta kashe a kiwon lafiya.” – Chaudhuri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministar kudi
Ministar kudin Najeriya, Zainab Ahmed Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

...A Yunin 2022 za mu janye hannunmu - Minista

Ministar tattalin kudi, tsare-tsare da kasafi, Zainab Ahmed ta yi jawabi a wajen taron, tace gwamnatin tarayya ta sa tallafin fetur a cikin kasafin ta na 2022.

Zainab Ahmed ta bayyana cewa a lissafin da aka yi, za a biya tallafin mai har watan Yunin 2022.

“A kasafin kudin 2022, mun cusa tallafin ne a farkon shekarar kurum. Muna kokarin janye hannunmu tsaf daga sha’anin mai da gas.” – Ahmed.

Read also

Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba – Tukur Buratai

Ahmed tace yin hakan zai sa Najeriya ta adana wasu kudi a asusunta na kudin kasashen ketare. Sannan wannan zai sa gwamnati ta samu kudi sosai daga mai.

Shugaban majalisar masu ba shugaban kasa shawara a kan harkar tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami yace tun ba yau ba, ya so a janye tallafin mai a kasar.

Mutane sun gamsu da mu - APC

Kwanaki aka ji sakataren Jam’iyyar APC na rikon kwarya, John Hames Akpanudoedehe yace hankali kwance za su ci zaben shugaban kasa a zaben 2023.

Sanata John Akpanudoedehe ya bayyana haka da yake nada kwamitocin sauraron korafin zabukan APC. Akpanudoedehe yace mutane sun natsu da APC.

Source: Legit

Online view pixel