Jerin Sunayen Tsaffi da Sabbin Limaman Masallacin Harami Na Makka

Jerin Sunayen Tsaffi da Sabbin Limaman Masallacin Harami Na Makka

A cikin addinin Musulunci, kalmar "Imam" tana nufin jagoran masallata, kuma ana zabar limaman Masallacin Harami ne bisa iliminsu na Musulunci, da takawa, da kwarewarsu wajen karatun Alqur'ani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Duk da cewa kun riga kun san manyan limaman Masallacin Harami, watakila ba ku san bayanai game da tsaffin limaman masallacin ba, da irin ayyukan da suke gudanarwa.

Jerin sunayen tsaffi da sabbin limaman Masallacin Harami.
Jerin sunayen tsaffi da sabbin limaman Masallacin Harami. Hoto: @HaramainInfo
Asali: Twitter

A halin yanzu, Khateeb kuma babban limamin masallacin Al Haram shine Sheikh Abdul Rehman Al Sudais, kamar yadda The Pilgrim ta ruwaito a 2023.

Shafin WikiPedia ya zayyana tsaffi da sabbin limaman Masallacin Harami, wanda Legit Hausa ta tattara bayanansu a kasa:

Jerin tsaffin limaman Masallacin Harami

Abdullah Al-Khulaifi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nada Abdullah Al-Khulaifi limami kuma Khateeb na Masallacin Harami daga 1953 har zuwa rasuwarsa a shekarar 1993.

Kara karanta wannan

FAAN, CBN: Yadda muka yi da Sanata Ndume da ya kira ni a waya da dare - Okupe

1. Ahmad Khatib

Shaikh Ahmad Khatib al-Minangkabawi ya kasance shugaban (limami) na mazhabar Shafi'iyya a masallacin Makkah (Masjid al-Haram). Ya rasu a Makka a ranar 9 ga Oktoba 1915.

2. Ali bin Abdullah Jaber

Ali bin Abdullah Jaber, ya kasance limamin Masallacin Harami daga 1981 zuwa 1983, kuma ya kasance bakon limami a watan Ramadhan na shekarar 1986 zuwa 1989.

3. Umar Al-Subayyil

Umar Al-Subayyil ya kasance limami kuma Khateeb daga 1993 har zuwa 2002, ya rasu a shekara ta 2002.

4. Mohammad Al Subail

Muhammad bin Abdullah Al-Sabil ya kasance limami kuma mai wa'azi a Masallacin Harami na tsawon shekaru arba'in da hudu.

Ya kuma kasance mamba a majalisar manyan malamai, kuma mamba a majalisar Fiqhu ta Musulunci, kuma shugaban al'amuran Masallacin Harami da Masjidul Nabawi, kuma shugaban kwamitin Al-Haram na kasar Saudiyya.

5. Abdullah Al-Harazi

Abdullah Al-Harazi, ya kasance tsohon shugaban majalisar Saudiyya al-Shura, kuma ya yi limanci a Masallacin Harami.

Kara karanta wannan

Atiku ya jefawa Gwamnatin Tinubu zafafan tambayoyi 5 kan bashin $3.3bn da aka ci

6. Ali bin Abdur-Rahman Al-Huthaify

Ali bin Abdur-Rahman Al-Huthaify ya kasance bakon limami a watan Ramadana na shekarar 1981, 1985-1986, 1988-1991, a yanzu kuma shi ne babban limamin masallacin Annabi.

7. Salah ibn Muhammad Al-Budair

Salah bn Muhammad Al-Budair, ya jagoranci Sallar Tarawihi a cikin Ramadanan shekarar 2005 da 2006, a yanzu kuma shi ne mataimakin babban limamin masallacin Annabi.

8. Adil al-Kalbani

Adil al-Kalbani malamin addinin Musulunci ne dan kasar Saudiyya wanda ya kasance limamin babban masallacin Makkah a shekara ta 2008, lokacin da sarki Abdullah ya zabe shi don jagorantar sallar tarawihi a masallacin.

9. Saleh Al-Talib

Sheikh Saleh bin Mohammed Al Talib malamin Saudiyya ne, mai wa'azi, limami, Khatib kuma alkali da ake tsare da shi tun watan Agustan 2018 saboda sukar gwamnati.

10. Khalid al Ghamdi

Khalid al Ghamdi ya yi ritaya a matsayin limami kuma katibi na Masallacin Harami a watan Satumba 2018.

Kara karanta wannan

Dangote zuwa Otedola: Masu kudin Afrika 20 da adadin Dalolin da suka mallaka a 2024

11. Saud Al-Shuraim

Saud Al-Shuraim, an nada shi limami kuma Khateeb a shekarar 1992 kuma yanzu ya yi murabus a 2022.

Jerin sabbin limaman Masallacin Harami

1. Abdul-Rahman Al-Sudais

Abdul-Rahman Al-Sudais, an nada shi limami kuma Khateeb a shekara ta 1984.

2. Salih bin Abdullah al Humaid

Salih bin Abdullah al Humaid, an nada shi limami kuma Khateeb a shekara ta 1984.

3. Usama Abdul Aziz Al-Khayyat

Usama Abdul Aziz Al-Khayyat, an nada shi limami kuma Khateeb a shekarar 1998.

4. Abdullah Awad Al Juhany

Abdullah Awad Al Juhany, an nada shi limami a shekarar 2007 da kuma Khateeb a shekarar 2019.

5. Mahir Al-Muayqali

Mahir Al-Muayqali, an nada shi limami a shekara ta 2007, kuma an nada shi Khateeb a shekara ta 2016.

6. Yasser Al-Dosari

Yasser Al-Dosari, an nada shi limami a shekara ta 2014.

7. Bandar Baleelah

Bandar Baleelah, an nada shi limami a shekara ta 2013, kuma an nada shi Khateeb a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Rikici Tsakanin Boko Haram Da ISWAP Ya Yi Ƙamari Yayin Da Suka Kashe Juna a Sabon Rikici

8. Faisal Jameel Ghazzawi

Faisal Jameel Ghazzawi, an nada shi limami kuma Khateeb a shekara ta 2008.

An gano zuriyar Sarkin Saudiyya da ta fi Musk, Gates arziki

A wani labarin kuma, wani rahoto ya tabbatar da cewa dukiyar da zuriyar Sarkin Saudiyya ta mallaka ta nunka wacce Bill Gates da Elon Musk suka mallaka har sau hudu.

An ruwaito cewa zuriyar ta mallaki dalar Amurka tiriliyan 1.4 kwatankwacin Euro tiriliyan 1.1 yayin da Elon Musk ke da dala biliyan 241.6 shi kuma Bill Gates ke da dala 119.9

Asali: Legit.ng

Online view pixel