Hukumomin Gwamnati Da Suka Bada Kyauta Ga Matar Da Ke Tashi 4.50 Na Asuba Don Yi Wa Mijinta Girki

Hukumomin Gwamnati Da Suka Bada Kyauta Ga Matar Da Ke Tashi 4.50 Na Asuba Don Yi Wa Mijinta Girki

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wasu hukumomin gwamnati sun shiga jerin wadanda suka rika bada kyauta ga wata yar Najeriya, MumZee, @_Debbie_OA, wacce aka caccaka a kafar X bayan ta wallafa rubutu cewa tana tashi karfe 4.50 na asuba a kullum don yi wa mijinta girki.

Matar wacce ta samu kyautan kudi fiye da naira miliyan 5 daga masu amfani da yanar gizo tana ta tashe a yan kwanakin nan.

Hukumomin Gwamnati Da Suka Bai Wa MumZee Kyauta
NNPCL, NITDA da OYSHIA sun bada kyauta ga MumZee, matar da ke tashi da asuba tana yi wa mijinta girki. Hoto: @_Debbie_OA, @NITDANigeria
Asali: Twitter

Ta wallafa cewa ta fara tashi karfe 4.50 na asuba a kullum don yi wa mijinta girki ne bayan ya fada mata wata abokiyar aikinsa ta kawo cokali biyu tare da abincinta domin su ci tare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bidiyon yadda limami ya rasu yana tsaka da jan sallah a masallaci ya dauki hankali

"Na saba kasalar tashi in dafa masa abincin rana. Amma ranar da ya fada min wata abokiyar aikinsa ta kawo cokali biyu domin su ci tare shine ranar da saka kararrawa na tashi karfe 4.50 na asuba," ta wallafa.

Wasu mata a kafar na X sun rika sukar abin da ta yi.

Daga cikinsu, UjuAnya, ta rubuta:

"Wato kina cewa kina tashi kafin alfijir ya fito ta dafa wa baligi abinci, don kada ya roki abokan aikinsa abinci kuma ya 'kwanta' da wani saboda dumamen shinkafa da kaza."

Sai dai, wannan sukar ya zama alheri ga MumZee, domin mutane da dama sun yunkuro sun kare ta, suka tara mata kudi da kuma kayayyaki da dama saboda hidimar da ta ke yi wa mijinta.

Hukumomin gwamnati da suka yi wa MumZee kyauta

A yayin da yan Najeriya da dama ke mata kyauta da mijinta, wasu hukumomin gwamnati suma sun mata ruwan kyaututuka a ranar Asabar 6 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Bayan cewa bai son a kai masa ziyara, Buhari ya yi kyautar galleliyar mota ga dan a mutunsa

Ga wadanda suka bada kyauta ga MumZee:

Hukumar Cigabar Sadarwa ta Kasa (NITDA) ta bai wa MumZee da mijinta kyautar kwamfuta (laptop) da data na shiga intanet na shekara daya.

Hukumar ta rubuta:

"Barka dai @_Debbie_OA, labarin soyayyar ki da juriya ya ratsa zuciya, kuma muna son baki kyautar laptop guda biyu da data na shiga intanet na shekara 1 ke da mijinki.
"Munyi hakan ne don tabbatar Mummy Zee ta shiga tafiyarmu ta #DigitalNigeria da #Tech4Women. Fatan Alheri!."

OYSHIA ta bai wa MumZee inshoran lafiya

Hukumar Inshora ta Jihar Oyo (OYSHIA) ita ma a ranar Asabar ta bai wa Mumzee da iyalanta inshoran lafiya a karkashin shirin inshora na jihar.

"@_Debbie_OA
"Halayenku masu kyau da dabi'a na gari a aurenki ya ja hankalinmu, kuma muna son mika godiyarmu. A matsayin tukwici na sha'awarmu, muna son ba ki da iyalanki inshoran lafiya na iyali a karkashin Inshora na jihar Oyo," Hukumar ta wallafa a X.

Kara karanta wannan

Matashi ya ba budurwarsa ta shekaru 7 naira miliyan 5 don ta bari ya auri wata daban, ta yi martani

NNPCL ta bai wa MumZee katin shan man fetur na N200,000

Kamfanin Tace Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya bai wa MumZee katin shan man fetur na N200,000.

"Barka dai @_Debbie_OA, muna kaunar labarinki na soyayya mai kayatarwa, kuma muna son ba ki katin shan man fetur na N200,000 da za ki iya amfani da shi a gidajen manmu fiye da 900 a Najeriya.
"Wannan zai tabbatar MumZee na da karfin yau da na gobe," kamfanin man ya wallafa a X.

Asali: Legit.ng

Online view pixel