Yadda Aka Samu Digirin Dakta Da Marigayi Sheikh Ja’afar Adam a Jami’ar Kasar Waje

Yadda Aka Samu Digirin Dakta Da Marigayi Sheikh Ja’afar Adam a Jami’ar Kasar Waje

  • Ismail Hashim Abubakar dalibin ilmi ne da ya yi karatun digiri a jami’ar Mohammed V a Morocco
  • Abin da wannan Bawan Allah ya yi bincikensa a kai shi ne da’awa da aikin Shaykh Ja’far Mahmud Adam
  • Shahararren malamin ya rasu a 2007 a sakamakon harbin bindiga da miyagu su ka yi masa ya na sallah

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Ismail Hashim Abubakar ya yi hira da Daily Reality bayan kammala digirinsa na uku watau PhD a kan harkar addinin musulunci a ketare.

Ismail Hashim Abubakar ya yi karatunsa ne a jami’ar Mohammed V da ke Rabat, ya kuma yi bincike game da Shaykh Ja’far Mahmud Adam Daura.

Dalibin ilmin ya bayyana cewa abin da ya biyo bayan rikicin Boko Haram ya tunzura shi yin bincike game da shahararren malamin musuluncin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Abba, Abokan Arziki Sun Tuna da Dadiyata Bayan Shekaru 4 da Bacewa

Ja’afar Mahmud Adam
Ismail Hashim Abubakar da Ja’afar Mahmud Adam Hoto: dailyrealityng.com
Asali: UGC

Ja’afar Mahmud Adam da Boko Haram

Nazarin da aka yi ya tabo alakar Marigayi Ja’far Mahmud Adam da Mohammed Yusuf, ya fayyace dangatakar shehin malamin da kungiyar ta’addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Binciken da Ismail Abubakar ya yi, ya nuna Mohammed Yusuf ya yi karatu a wajen Sheikh Ja’far Adam amma bai yi zurfin da zai zama magajinsa ba.

Wani bangaren ilmi da binciken ya ba muhimmanci shi ne ra’ayin shahidin malamin a kan dabbakar da shari’ar addinin Musulunci a Arewacin Najeriya.

A hirar da aka yi da shi, dalibin ya shaida yadda ya yi nazarin alakar Musulmai da Kiristoci – daga sabanin da ake tsakaninsu zuwa inda aka yi tarayya.

Wanene Ja'afar da gwagwarmayarsa

Wanda ya karanta wannan bincike mai kundi hudu, zai ga yadda marigayin ya yi yarintarsa har ya samu tafiya jami’ar musulunci da ke Madina a Saudi.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Shugabar Masu Addinin Gargajiya Gidan Yari a Ilorin Kan 'Cin Mutuncin' Shehin Malamin Islama

A binciken akwai irin aikin yada addini da Sheikh Ja’afar Adam ya yi a lokacin rayuwarsa musamman a garuruwan Kano, Bauchi da Maiduguri.

Binciken ya kunshi sukar da malamin ya yi wa masu mulki da gwamnatoci da matsayarsa kan gawurtattun ‘yan siyasa da wasu manya a zamaninsa.

Kafin ya yi nasarar kammala binciken nan, sai da Ismail Abubakar ya saurari karatuttuka, hudubobi da laccocin malamin, bayan hira da jama’a.

An ji labari kotun daukaka karar shari'a za ta sake duba hukuncin da aka yi a kotun shari’ar musuluncin Jigawa wajen rabon gadon tsohon Sarkin Dutse.

Asiya Nuhu Sanusi ta ce Sarkin ya ba ta kyautar gida, amma aka raba sauran gado da shi. Matar tsohon Sarkin ta ce kishiyoyinta sun tsira da gidajensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel