"Yarinyar Kirki": Bayan Shekara Daya a Kasar Waje, Budurwa Ta Turo Kudi Gida An Ginawa Mahaifiyarta Gida

"Yarinyar Kirki": Bayan Shekara Daya a Kasar Waje, Budurwa Ta Turo Kudi Gida An Ginawa Mahaifiyarta Gida

  • Wata budurwa mai shekara 25 a duniya wacce ta kwashe shekara ɗaya a ƙasar Koriya ta gwangwaje mahaifiyarta da babbar kyauta
  • Budurwar ta riƙa turo kuɗi zuwa gida sannan ta ginawa mahaifiyarta katafaren gida wanda hakan ya burge mutane da dama
  • Mutane da dama da suka kalli gidan sun yi fatan cewa su ma wata rana kakarsu za ta yanke saƙa su yi wa iyayensu irin wannan aikin arziƙin

Wata mahaifiya ta fara cin gajiyar ɗiyar da ta haifa bayan ta gama wahala da ita. Bayan kwashe shekara ɗaya da wata biyu a ƙasar waje, sai ta turo da kuɗaɗe zuwa gida.

An yi amfani da kuɗin da ta ke turowa wajen gina ƙayataccen gida mai kyau ga mahaifiyarta.

Budurwa mai aiki a kasar waje ta ginawa mahaifiyarta gida
Budurwar ta gwangwaje mahaifiyarta da gida Hoto: @lusanda_jiba
Asali: TikTok

Budurwar mai shekara 25 a duniya wacce malamar makaranta ce wacce ke amfani da sunan (@lusanda_jiba) a TikTok ta yi alfahari da abinda ta yi wa mahaifiyarta a ƴan ƙananan shekarun da ta ke da su.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Farmaki Wasu Kauyuka a Jihar Bauchi, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah Masu Yawa

Budurwa ta ginawa mahaifiyarta ƙayataccen gida

Wani bidiyon da ta sanya a manhajar TikTok ya nuna yadda ginin gidan yake gudana tun daga farko har zuwa matakin yin rufi. Mahaifiyar kuma cike da murna har nuna ta aka yi a gaban gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Budurwar wacce ƴar ƙasar Afirika ta Kudu ce ta bayyana cewa ta bar komai inda ta koma ƙasar Koriya domin yin aiki.

A kalamanta:

"Wannan na ki ne mahaifiyata, nagode bisa goyon bayan da kika ba ni."

Ga kaɗan daga cikin sharhin da aka yi akan bidiyon a nan ƙasa:

Anon Ymous ya rubuta:

"Ga waɗanda su ke mamakin meyasa mutane ke neman aiki s ƙasar waje, ga dalilin nan."

Hunadiee ya rubuta:

"Abin ban sha'awar shi ne za ki dawo gida ki tarar da shi fiye da yadda ki ka bar shi. Kin yi hakan."

Kara karanta wannan

"Ya Daina Nuna Mun Soyayya" Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Raba Auren Kuma Ta Umarci Mijin Ya Riƙa Biyanta N30,000

Mokgadi Ramalepe ya rubuta:

"Tabbas ke gwarzuwar mace ce."

Andiswa Optimistic F ta rubuta:

"Ina matuƙar alfahari da ke."

Matashiyar Budurwa Ta Samu N1.2bn Cikin Wata Shida

A wani labarin kuma, wata budurwa ta samu tagomashi bayan ta duƙufa harkar kasuwanci gadan-gadan domin tsira da mutuncinta.

Budurwar ta samu N1.2bn a cikin wata shida bayan ta kasa ci gaba da karatu a makaranta, inda ta tattara ƴan komatsanta ta dai na zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel