Abin Mamaki: An Hangi Dan Shugaba Tinubu Da ‘Power Bank’ A Aljihunsa A Villa, Hoton Ya Jawo Mahawara

Abin Mamaki: An Hangi Dan Shugaba Tinubu Da ‘Power Bank’ A Aljihunsa A Villa, Hoton Ya Jawo Mahawara

  • Hoton dan shugaban kasa, Bola Tinubu, Seyi Tinubu ya kawo mahawara a kafar sadarwa ta intanet
  • An gano hoton Seyi sanye da bakaken kaya ya na rike da waya a hannunsa a fadar shugaban kasa
  • Abin da yafi ba wa mutane mamaki shi ne ganin tukunyar cajin waya a aljihunsa kuma a Villa

FCT, Abuja - Dan Shugaba Tinubu, Seyi Tinubu ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta zamani bayan ya wallafa hotonsa a fadar shugaban kasa.

Ya wallafa hotonsa a shafin Instagram yana sanye da wasu bakaken kaya da waya a hannunsa.

Hoton dan shugaba Tinubu, Seyi ya jawo rudani a intanet
Hoton Dan Shugaba Tinubu Da ‘Power Bank’ A Aljihunsa A Villa. Hoto: @StFreakingKezy.
Asali: Twitter

Abin da ya dauki hankulan mutane shi ne yadda aka ga tukunyar cajin waya 'Power Bank' a aljihunsa.

Wasu daga cikin mutane sun bayyana cewa watarana shi zai mulki kasar, yayin da wasu ke mamakin ganin Power Bank a fadar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta bayyana cewa babu tabbacin tukunyar cajin waya ne a aljihunsa ko kuma waya ce ta lasifikar kunne.

Masu ta'ammali da kafar Instagram sun tofa albarkacin bakinsu:

official2baba:

"GBAM!

saidu6214:

"Me ya faru babu wuta a fadar shugaban kasa, naga Power Bank a aljihunsa.

ijoba_yagi_:

"Naga alamun zaka mulki kasar watarana, ku rubuta ku ajiye, naga alamu ko ku yarda ko kada ku yarda.

fomajoe:

"Zai fi kyau idan baka sa Power Bank ba a aljihunka kana yawo don ba wa wayarka wuta, A samar da wuta a Najeriya.

Wani matashi Pastor Okezie J Atani @StFreakingKezy ya sake wallafa hoton a kafar Twitter inda ya rubuta kamar haka:

"Dan fari ga shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, @STinubu"

Yayin da masu ta'ammali da kafar Twitter suka ce watakila yana amfani da Power Bank din ne ba wai don babu wuta a fadar shugaban kasa ba.

Masu ta'ammali da shafin Twitter sun tofa albarkacin bakinsu:

@Nawas_masood:

"Gwamna jihar Lagos mai zuwa.

@Vikky4_:

"Dan shugaban kasa da amfani da Power Bank, toh ya yi kyau.

@PaulOmozee:

"Wahala!!!!

@Logic_harris:

"Dan babansa. Ina son samun 'da kamar Seyi @STinubu.

Dukkansu Makafi Ne: Ba Sauki, Amma a Haka Na Rene Su, Inji Uwar Makafi 11

A wani labarin, Wata mata ta bayyana yadda ta haifi 'ya'ya 11 dukkansu makafi kuma ita ta ke kula da su.

Matar mai suna Agnes Nespondi ta bayyana yadda ta ke son yaranta, ta ce tun lokacin da aka haide su a haka suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel