Dukkansu Makafi Ne: Ba Sauki, Amma a Haka Na Rene Su, Inji Uwar Makafi 11

Dukkansu Makafi Ne: Ba Sauki, Amma a Haka Na Rene Su, Inji Uwar Makafi 11

  • Wani faifan bidiyon wata mata ya yadu inda ta bayyana yadda ta haifi yara 11 dukkansu makafi
  • Matar mai suna Agnes Nespondi ta ce dukkan yaran a haka ta haifesu gaba daya tun farko
  • Ta ce lokacin da ta haifi yaronta na farko ta yi tunanin sauran ba haka za su zo ba kamar na farkon

Wata mata ta bayyana yadda ta haifi yara 11 dukkansu makafi a kafar sadarwa ta zamani, ta ce ita ta ke kula da su.

A wani faifan bidiyo da AfrimaxTV ta wallafa, matar mai suna Agnes Nespondi ta ce ta haifi yaran tun daga haihuwar su makafi.

Matar da ta haifi yara makafi 11, ta ce ita ta ke kula da su
Uwar Yara Makafi 11 Ta Bayyana Halin Da Ta Ke Ciki. Hoto: AfrimaxTV.
Asali: Youtube

Ta bayyana yadda ta haifi jaririnta na farko makaho, inda daga bisani ta haifo sauran 10 duka makafi.

Ta ce bayan ta haifi biyu makafi, ta yi addu'an samun masu ido a gaba don su kula da guda biyun da ba sa gani.

Kara karanta wannan

Inda Ranka: ’Yar Najeriya Ta Yi Dabara a Kasar Turai, Ta Kama Siyar da Dafaffen Abincin Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dukkan makafin 'ya'yan nata sun girma, sai dai guda biyu 'yan kanana na karshe

'Ya'yan nata dukkansu sun girma, sai dai guda biyu na karshe su ne kawai 'yan kanana a cikin yaranta, cewar Legit.ng.

A faifan bidiyon mai ratsa zuciya, ta nuna yadda ta ke son yaran nata wadanda ba za su iya taimakon kansu ba.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Ta bayyana yadda ta ke ji a rayuwa kamar tafi kowa rashin sa'a a duniya saoboda wannan jarabawa.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da bidiyon:

Subhanallah:

"Allah ka yaye mana abin da ba zamu iya dauka ba, Ameen."

Adusky1:

"Akwai matsalar rashin lafiya da ya kamata a bincika."

Realhabibaibrahim:

"Allah ka yafe mana, yayin da muka ki gode maka yadda ya dace, ka yafe mana lokacin da muke kokwanton ni'imarka."

Kara karanta wannan

"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

Ademigunle:

"Ubangiji ka yafemin duk lokacin da nake mita akan yarana wadanda kullum nasan kara gyaruwa suke."

Dr._kn added:

"Watakila akwai mayu a harkan, ku tina shirin wasan kwaikwayo na 'alani pamileku' abin ya faru da gaske."

Iam_sabsab:

"Waye ya kula cewa duka yaran maza ne, oh ubangiji wa zai taimaka idan ta mutu."

Zeextwax:

"Wannan akwai shafar aljanu a ciki."

Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

A wani labarin, wata mata da ke rayuwa a Saudiyya ta nuna bacin ranta a wani faifan bidiyo bayan ganin halin da 'yarta ke ciki.

Matar ta ce ko wane wata ta na turo makudan kudade don kula da ita, amma ashe ba ta samun kulawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel