An Dauke Bobrisky Daga Gidan Gyaran Halin Ikoyi Inji Jami'in Kurkuku

An Dauke Bobrisky Daga Gidan Gyaran Halin Ikoyi Inji Jami'in Kurkuku

  • Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCS) ta tabbatar da dauke Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky daga gidan gyaran hali na Ikoyi zuwa Kirikiri
  • Bayanan da aka samu daga jami'in hukumar sun tabbatar da cewa an canja masa wurin zaman ne cikin karshen makon da ya gabata
  • Har ila yau jami'in ya kuma bayyana dalilan da suka sa hukumar ta canja masa wurin zama daga Ikoyi zuwa Kirikiri

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bayanan da suke fitowa sun bayyana cewa hukumar kula gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCS) ta mayar da Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky Kirikiri daga Ikoyi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin rijiyoyin mai kan rashin biyan haraji

Bobrisky
Jami'in kula da gidan gyaran halin ya ce an canjawa Bobrisky wurin zaman ne saboda tsaro. Hoto: Bobrisky
Asali: Facebook

An yanke wa Bobrisky hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali ne bisa laifin cin zarafin Naira.

Jaridar Leadership ta tabbatar da cewa sabon rahoton ya sabawa rahotannin da ke cewa ana tsare da Bobrisky ne a gidan gyaran hali na Ikoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kai Bobrisky Kirikiri?

Jami’in hukumar gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCS) ne ya shaida cewa a halin yanzu ana tsare da Bobrisky ne a gidan gyaran hali na Kirikiri.

Wannan jam'in ya kuma kara da cewa an dauke shi ne tun karshen makon da ya gabata zuwa Kirikiri, cewar jaridar Tribune

Meyasa aka canja masa gidan maza?

Ma'aikacin kurkukun ya tabbatar da cewa ka'ida ce a kai shi Kirikiri tun da gidan gyaran hali ne marar cinkoso.

Ya kara da cewa, saboda dalilai na tsaro, an kai Okuneye inda zai samu nutsuwa har ya cika wa’adinsa na wata shida.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da shahararren dan kasuwa Cubana bisa zargin cin zarafin Naira

Idan dai za a iya tunawa, Mai shari’a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya da ke Legas ne ya yanke wa Bobrisky watanni shida a gidan gyaran hali.

Da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu, alkalin ya ce hukuncin zai hawu kan duk wanda aka kama da cin zarafi da lalata naira.

Karin rahotanni sun tabbatar da cewa an kai mai laifin ne zuwa gidan yari na maza kuma za a kula da shi a matsayin fursuna ba tare da bambanci ba.

Bobrisky ya ce shi namiji ne

A wani rahoton kuma, kun ji cewa shahararren dan daudu mai suna Idris Okuneye, da aka fi sani da Bobrisky, ya amsa cewa shi namiji ne ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu.

Ya amsa hakan ne a lokacin da mai shari'a Abimbola Awogboro ya tambayesa jinsinsa kafin yanke masa hukunci bisa zarginsa da wulakanta takardun Naira a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel