Gwamnan Gombe Ya Yi Ta’aziyyar Mutumin da Ya Rasa Iyalansa 6 a Hatsarin Mota

Gwamnan Gombe Ya Yi Ta’aziyyar Mutumin da Ya Rasa Iyalansa 6 a Hatsarin Mota

  • Mai Dalan Gombe, Alhaji Ahmed Abubakar, ya rasa iyalansa guda 6 a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su
  • Hatsarin ya ritsa da su ne a kan babbar hanyar Azare zuwa Gombe a jiya Lahadi, 14 ga watan Afrilu
  • Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi ta'aziyya wa Mai Dalan Gombe ya kuma ce mutuwar ta shafi al'ummar Gombe baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamna jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya, ya yi ta'aziyya wa maidalan Gombe da ya rasa iyalansa guda shida a hadarin mota.

Gwamnan ya yi ta’aziyyar ne a wani sako da mataimakinsa na musamman a harkar yada labarai, Isma'ila Uba Misilli, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

Inuwa Yahaya
Iyalan Mai Dalan Gombe maza da mata su 6 sun rasu ne a hanyar Azare sanadiyar hatsarin mota. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Asali: Facebook

'Yan uwan Mai Dalan Gombe sun rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Azare zuwa Gombe a jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka rasun sun hada da 'ya'yan Mai Dalan Gombe da 'ya'yan kaninsa.

Wadanda suka halarci jana'izar

Gwamna Inuwa da ya halarci Sallar Jana’izar tare da Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dr Abubakar Shehu Abubakar III, da sauran daruruwan jama’a, ya yi nuni da cewa, rashin ‘yan uwa a irin wannan mummunan yanayi abu ne mai matukar muni.

Ya ce al’ummar Gombe gaba daya wannan abin bakin ciki ya shafa, ba iyalin Mai Dala kawai ba.

Ta'aziyyar gwamnan Gombe

"Muna mika ta'aziyyarmu ga Maidalan Gombe da daukacin 'yan uwa da suka rasu a wannan lokaci mai matukar wahala.
Rasuwar 'yan uwa 6 a cikin irin wannan mummunan hatsarin mota ba kawai babban rashi ne ga dangin ku ba, har ma ya shafi daukacin al'ummar Gombe baki daya."

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya tafka rashi har 2 a rana 1 kwanaki kadan bayan bikin sallah

"Kalmomi ba za su iya bayyana bacin ran da ku da masoyanku ku ke ciki ba. Ku sani cewa kuna cikin addu'o'inmu yayin da ku ka samu kan ku cikin wannan yanayi mai raɗaɗi".

-Inuwa Yahaya

Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya gafarta musu kurakuransa, ya saka musu da Aljannar Firdausi.

Anyi mummunan hatsarin mota a Ondo

Kun ji cewa wani hatsarin mota da ya auku a jihar Ondo ya yi sanadiyyar fasinjoji mutum hudu bayan motarsu ta faɗa rami.

Wasu mutum 10 kuma sun samu raunuka bayan motar bas ɗin ta ƙwace ta faɗa cikin ramin a safiyar ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel