Kina da Dakika 60: Budurwa Ta Kwashi Kaya Kyauta a Kanti Na Makudan Kudade Fiye da N1m

Kina da Dakika 60: Budurwa Ta Kwashi Kaya Kyauta a Kanti Na Makudan Kudade Fiye da N1m

  • An bai wa wata budurwa damar diban kaya kyauta a wani babban kanti amma a cikin dakika 60 kawai
  • Budurwar ta bai wa mutane mamaki inda ta wuce wurin da ake ajiye manyan kaya ta kwashe abin da ya kai N1m
  • Mutane da dama sun yabi yarinyar ganin yadda take da sauri da kuma sanin irin kayan da za ta diba

Wata budurwa ta ba da mamaki inda ta kwashi kaya da dama a cikin dakika 60, a wani babban kanti bayan an ba ta daman diba kyauta.

An fada mata cewa duk abin da za ta kwasa a cikin abin diban kaya a wannan lokaci kyauta ne.

Budurwa ta cika kwando da kaya a babban kanti har N1m
Budurwa Ta Kwashi Kaya Kyauta a Kanti Na Makudan Kudade. Hoto: @zoomlifestyle.
Asali: TikTok

Lokacin da aka fara kirga lokaci, budurwar ta yi sauri ta fara tattara abubuwa a babban kanti na ShopRite, wadanda suka hada da fanka da abin girki.

Irin manyan kayayyakin da budurwar ta kwasa

A wani faifan bidiyo da @zoomlifestyle ya wallafa, budurwar da kuma dauki kwantena na yin kankara da kuma abin gashi da fankar kasa da kuma abin girki yayin da ta ke daukar komai bibbiyu a kanti.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu ta’ammali da kafar sada zumunta sun yabi yarinyar ganin yadda ta ke da sauri da kuma irin kalar kayan da ta dauka.

Akalla kayan da ta kwasa ya kai kudi har N1m a wannan shagon wanda aka mata alkawarin kyauta ne idan ta dauka a cikin dakika 60.

Ku kalli faifan bidiyon a kasa:

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane kamar haka:

Horlanrewaju Homotayo Zainab:

"Ta fahimci aikin da aka saka ta.”

Cakes&treats_bykuddy:

“Daman ta dade tana jiran wannan rana a rayuwarta.”

Purplekitty:

“Dan Allah a ina ne za a sake yin haka.”

Victoria:

“Ina neman wanda zai min haka.”

ChizzyNancy:

“Ban taba yin wannan wasa ba, za ku bata wasan, yanzu za su tsaida ita.”

Omotolani:

“Ku taimaka ku zo kantin Circle mana.”

Buddy said:

“Yarinya mai wayo, ba kamar sauran mata ba da abinci kawai suka sani, amma wannar ‘yar Naija ne ko.”

user9842167966581:

“Ai nikam wurin Laptop zan je da Gucci.”

Chidera:

“Ku taimaka kuzo jami’ar Port Harcourt, na yi alkawari ba zan kai hari babban kanti ba.”

Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata

A wani labarin, wata mata da ke rayuwa a kasar Saudiyya ta shiga bakin ciki bayan ganin yadda 'yarta ta kasance.

Matar ta ce kowane wata ta na turo makudan kudade don kula da yarinyar amma ba ta ga sauyi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel