"Sai Da Na Kwashe Shekara 13", Wani Matashi Dan Najeriya Ya Kera Janareto Mara Kara Wanda Baya Amfani Da Fetur

"Sai Da Na Kwashe Shekara 13", Wani Matashi Dan Najeriya Ya Kera Janareto Mara Kara Wanda Baya Amfani Da Fetur

  • Wani matashi wanda ya kammala karatun sa a fannin kwamfuta ya ƙera janareto mara ƙara wanda baya amfani da man fetur
  • Matashin wanda yake tuƙa achaɓa ya bayyana cewa sai da ya shafe shekara 13 yana ƙoƙarin haɗa wannan janareton
  • Yana buƙatar waɗanda za su ɗauki nauyin sa ya samar da irin wannan janareton da yawa inda yace yana daɗin aiki

Oyekunle Michael, wanda ya karanci kimiyyar kwamfuta daga kwalejin Interlink Polytechnic, ya ƙirƙiro janareto mara ƙara wanda ba a sanya masa man fetur.

Matashin ɗan asalin jihar Oyo wanda ya ƙirƙiro wasu abubuwan da dama yace sai da yayi ta gwadawa har sau sha biyar, babu nasara kafin daga ƙarshe ya samu nasara a shekarar 2022.

Janareto
"Sai Da Na Kwashe Shekara 13", Wani Matashi Dan Najeriya Ya Kera Janareto Mara Kara Wanda Baya Amfani Da Fetur Hoto: Twitter/@bod_republic
Asali: UGC

A wani bidiyo da aka sanya a Twitter, matashin wanda ɗan achaɓa ne ya nuna yadda janareton yake aiki, wanda sai da ya kwashe shekara 13 yana ƙoƙarin ƙera shi saboda matsalar kuɗi.

Kara karanta wannan

"Ina Da Ikon Naɗa Duk Wanda Na So Har 29 Ga Mayu" Gwamnan PDP Ya Maida Martani

Michael a wata tattaunawa da Legit.ng ya bayyana cewa janareton baya gurɓata muhalli, yana da daɗin aiki, baya buƙatar gyara sosai kuma yana da inganci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Yana da inganci sosai kamar janareto mai amfani da man fetur. Wanda na haɗa yanzu yana ɗa ƙarfin 900 watts irin na ɗan ƙaramin janareto, kuma zai iya ɗaukar kayan wuta irin su TV, fanka, ƙwayaye, ya danganta da girman su."
"Zan iya ƙera mai ƙarfin 1kva har zuwa 20kva domin ba gida da ofis wuta idan na samu gudunmawa."

Michael ya bayyana cewa ya fara ne shekara goma sha uku da suka gabata lokacin da iyayen sa suka rabu.

"Na fara ne shekara 13 da suka gabata. Iyayena sun rabu, sannan sai wahala ta ƙaru akan mahaifiyata. Dole ta tura ni zuwa Ibadan na zauna a wajen yayan mahaifina."

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashin Ma'aikata, Abu Daya Kawai Ya Rage

"Muna shan doguwar tafiya kafin mu je makaranta. Ba wuta domin yin karatu, goge kaya, yin kallon finafinai da sauran su. Mutanen dake da janareto a lokacin sai sun yi tafiya mai nisa kafin su samo man fetur."
"Sai nayi tunanin haɗa janareto wanda zai iya aiki a koda yaushe ta yadda kowa zai samu wuta. Na gayawa malamin Physics ɗina game da hakan, sai yace kwarai zai yiwu idan zan iya haɗa injin da zai samar da wuta."
"Daga nan sai na fara aiki akan shi. Sai na gayawa wanda nake zaune a wajen shi inda ya nuna yaji daɗin wannan tunanin nawa amma ba kuɗin da zai iya taimaka min da su saboda ma'aikaci ne kuma manomi."
"Daga cikin ɗan abinda nake samu, na ɗauki nauyin karatun difloma ɗina a fannin kwamfuta sannan na kuma tara kuɗin da na haɗa samfurin janareto mara amfani da man fetur."
"Sau kusan 15 ina gwadawa babu nasara kafin daga ƙarshe nayi nasara a shekarar 2022, na kashe kusan dubu ɗari biyu da hamsin banda waɗanda na kashe lokacin da nake ƙoƙari ban yi nasara ba."

Kara karanta wannan

Malamin Addinin Musulunci Ya Dau Zafi Ya Bayyana Illar Makarkashiyar Hana Rantsar Da Tinubu

Yace yanzu yana buƙatar taimako ne domin ya samar da janareton da yawa, sannan zai iya ƙero manya sosai idan akwai kuɗi.

Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:

Bidiyon Wani Malamin Addini Na Huduba Cikin Harshen Igbo Ya Yadu Sosai

A wani rahoton kuma, wani malamin addinin musulunci ya ɗauki hankula sosai bayan bayyanar bidiyon sa yana huɗuba da harshen Igbo.

Abu ne dai wanda ba kasafai aka saba ganin hakan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel