Charterhouse Lagos: Kyawawan Hotunan Makarantar Firamare Mafi Tsada a Najeriya

Charterhouse Lagos: Kyawawan Hotunan Makarantar Firamare Mafi Tsada a Najeriya

  • Hotunan sabuwar makarantar firamare ta Charterhouse mafi tsada a Najeriya da aka kaddamar a Legas sun jawo cece kuce
  • Yadda aka yi ginin makarantar ya fita daban da irin wanda aka saba gani kuma da alama ta cancanci karbar N42m a kowace shekara
  • Sai dai da yawan ‘yan Najeriya sun soki tsadar kudin makarantar tare da mamakin abin da ya banbanta da sauran makarantun firamare

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Charterhouse Legas ta fitar da kyawawan hotunan gine-gine, dakunan karatu da alatun da ta zuba a sabuwar makarantar firamare da ta bude.

Makarantar firamaren tana kan titin Ogombo, Ogombo, Lekki, Legas, kuma ana ganin an bude ta ne kawai domin 'yayan masu kudi.

Kara karanta wannan

Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa

Kyawawan hotunan cikin Charterhouse Lagos, firamare mafi tsada a Najeriya
Rahotanni sun ce Charterhouse Lagos ita ce makarantar firamare mafi tsada a Najeriya. Hoto: Charterhouse Lagos
Asali: UGC

Charterhouse: Firamare mafi tsada a Najeriya

Charterhouse ta fitar da hotunan ne a shafinta na yanar gizo, kuma suna ci gaba da yaduwa a soshiyal midiya yayin da mutane ke bayyana ra'ayoyinsu kan kayatuwar makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ita ce makaranta mai zaman kanta ta Biritaniya ta farko a Yammacin Afirka kuma daya daga manyan makarantu mallakin Charterhouse.

Kudin shigar da yaro makarantar Naira miliyan biyu ne. Kudin makaranta kuwa Naira miliyan 42 ne, wanda hakan ya sa ta kasance makarantar firamare mafi tsada a Najeriya.

Kalli kyawawan hotunan makarantar firamare ta Charterhouse da ke Legas a nan shafin.

Charterhouse Lagos, makarantar firamare mafi tsada a Najeriya
Kyakkyawan hoton makarantar daga waje. Hoto: Charterhouse Lagos
Asali: Twitter

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan Charterhouse

Adeyemi Yekini ya ce:

"Ba da gaske suke neman kudin ba, ko Emefiele zai yi wahala wajen biyan wannan adadin kudin na tsawon shekaru 11 na karatun firamare da sakandare."

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Abubuwan da gwamnati ta shirya yi a bikin cikar Tinubu shekara 1 a mulki

Okwuchukwu Oparaku ya ce:

“Abin da kawai zai sa na biya wannan N42M din, idan kowa a gidanmu zai fara karatun Nursery a can har zuwa matakin digiri na uku, kuma idan sun kammala, za su dauki dukkaninsu aiki a makarantar."

Babatunde Francis ya ce:

"Kada mu yaudari kanmu, wannan makaranta ta hadu. Har na fara tunanin yadda zan saka 'yayana idan na haife su. Ubangiji ka rabamu da talauci."

Ajala A. Habib ya ce:

"Wata rana zan samu kudin da zan kai yarana can, da izinin Allah, amma yanzu dai zan kai su wani wuri mai rahusa."

Ibrahim Jamila ta ce:

"Kudin da zan yi amfani da shi wajen gina rijiyar burtsatse ga al'ummata, shi ne zan dauki dawainiyar yaro daya kacal?

“Idan kudin makarantar firamare da sakandare ya haura N500,000 ko N1m, to ba da ni ba."

Su wa ke iya karatu a Charterhouse?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani kwararre a kan al'amuran gudanarwa, Dr Dípò Awójídé ya ce kaso daya cikin al'umma ne ke iya kai 'ya'yansu irin wannan makarantar.

Sai dai Dr Awójídé na ganin wannan abin alfahari ne ganin cewa irin ta ce ta farko a nahiyar Yammacin Afirka kuma hakan zai kara daga darajar kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel