Aliko Dangote, Abdussamadu da cikakken jerin masu kudin Afrika 10 a yau da sana’arsu

Aliko Dangote, Abdussamadu da cikakken jerin masu kudin Afrika 10 a yau da sana’arsu

  • Duk da annobar COVID-19 da aka yi, dukiyar manyan Attajiran Afrika ta karu sosai ‘yan shekarun nan
  • Lissafin Forbes ya nuna masu kudin nahiyar Afrika sun mallaki dukiyar da ta kai fam $84.9b a karshen 2021
  • Aliko Dangote da wasu ‘Yan kasuwan kasar Masar da Afrika ta kudu su na cikin manyan masu kudi

A wannan rahoto da Forbes ta fitar, an gano su wanene wadanda suka fi kowa kudi a nahiyar Afrika da takaitaccen bayanin inda suka fito da sana’arsu.

1. Aliko Dangote

Har gobe Aliko Dangote ne wanda ya fi kowa kudi a Afrika. Rahoton Forbes ya ce Dangote ya na da $13.9bn a yanzu. Attajirin ya yi kudi ne da siminti da wasu harkokin.

2. Dangin Johann Rupert

Na biyu su ne Johann Rupert da ‘yan danginsa. Ana hasashen sun ba sama da Dala biliyan 11 baya. Rupert ya yi kudi ne da harkar tufafi da saide-saiden kaya.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

3. Nicky Oppenheimer

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nicky Oppenheimer su ne na uku a jerin da aka fitar a 2022. Da harkar ma’adanai da karafuna, dukiyar Oppenheimer mai shekara 76 ta kai Dala biliyan 8.7 a yau.

4. Nassef Sawaris

Attajirin Balaraben Misran nan, Nassef Sawaris yana biye da Nicky Oppenheimer da Dala biliyan 8.6. Sawaris ya gawurta a harkar gine-gine da kere-kere a Duniya.

Jerin masu kudin Afrika 10 a yau da sana’arsu
Masu kudin Afrika a 2022
Asali: UGC

5. Abdussamad Rabiu

Babban labarin shi ne zaburar Abdussamad Rabiu zuwa na biyar a sahun masu kudi. Ta harkar abinci, siminti da sauran kasuwanci ya mallaki Dala biliyan 7.

6. Mike Adenuga

Wani mutumin Najeriya da yake jerin bayan Dangote shi ne Mike Adenuga. Attajirin da ya mallaki Dala biliyan 6.7 yana sana’a da-dama daga ciki akwai sadarwa.

7. Issad Rebrab

Kasuwancin Issad Rebrab da danginsa ya yi kaimi, yanzu sun mallaki Dala biliyan 5.1 a Aljeriya. Attajirin ya yi kudi ne da harkar kasuwancin kayan abinci da sauransu.

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

8. Naguib Sawaris

Da Dala biliyan 3.4, Naguib Sawaris shi ne na takwas a masu kudin nahiyar Afrika. Sawaris wanda mutumin Masar ne ya samu dukiya ne daga harkar sadarwa.

9. Patrice Motsebe

Patrice Motsepe shi ne mutum na tara a sahun masu kudin Afrika. Forbes ta ce mutumin Afrikan ta kudu ya mallaki Dala biliyan 3.1 da harkar ma’adanai da karafuna.

10. Koos Bekker

A halin yanzu Koos Bekker shi ne ya rufe sahun farkon na mu. Bekker mai shekara 69 ya na da Dala biliyan 2.7 a banki a sanadiyyar harkar yada labarai da nishadi.

Aikin matatar Dangote

A makon nan ne aka ji shugaban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina ya kai ziyara zuwa matatar Aliko Dangote da ake kokarin karasawa a garin Legas.

Akinwumi Adesina ya yaba da wannan gagarumin aiki ma babban mai kudin Afrika. Mutane 38, 000 za su samu aiki, baya ga fetur da takin zamani da za a rika samu.

Kara karanta wannan

Sunaye Da Hotuna: Baƙaƙen Fata 5 Da Suka Fi Kudi a Duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel