Duk da ya samu Duniya, Gwamna ya tuna da mutumin da ya fara ba shi aikin kwandasta

Duk da ya samu Duniya, Gwamna ya tuna da mutumin da ya fara ba shi aikin kwandasta

  • Gwamna Samuel Ortom ya karrama mutumin da ya ba shi aikin yaron mota shekaru 40 da suka wuce
  • Samuel Ortom ya bayyana yadda Mnenge Mtemave ya fara dauko shi a matsayin karen motarsa
  • Yau wannan karen mota ya zama gwamna, don haka ya yi wa tsohon Mai gidansa sha tara na arziki

Benue - A ranar Litinin, 27 ga watan Disamba, 2021, gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya tuna da tsohon mai gidansa, Mnenge Mtemave da abokan aikinsa.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya karrama Mnenge Mtemave a dalilin tasirin da ya yi wa rayuwarsa a shekarun da suka wuce.

Mai girma Samuel Ortom ya yi amfani da lokacin bikin kirismeti, ya yi wa Mista Mnenge Mtemave da sauran abokan aikinsa a garejin garin Gboko sakayya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun sako sirikin Sanata Okorocha da suka cafke

Daily Post tace Gwamna Ortom ya karrama abokan aikin tsohon direban a gidansa da ke kauyen Ipav, garin Mbadim a karamar hukumar Gboko, jihar ta Benuwai.

Tarihin zaman Ortom a gareji

Gwamnan ya taba zama yaron mota a karkashin Mtemave lokacin da yake aiki a babban garejin na Gboko a karshen shekarun 1970s zuwa farkon shekarun 1980.

Gwamna Ortom
Ortom da tsofaffin direbobi Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ortom ya yi aikin yaron mota ne a lokacin da ya daina karatu yayin da yake makarantar firamare.

Da yake jawabi a wajen karrama tsohon mai gidan na sa, Ortom yace Mtemave ne ya fara dauko shi a matsayin yaron motarsa, daga baya kuma ya koya masa tuki.

Bayan nan Mista Mtemave ya maida Ortom wanda a yau ya ke gwamna, ya zama ma’ajin kudin da aka samu, ya kuma yarda ya rika kashe duk abin da yake bukata.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

A cewar Ortom, duk da damar da ya samu, sai ya nemi izinin mai gidansa kafin ya taba kudin.

Mtemave ya taki sa'a da kirismeti

Ubangiji ne ya nuna masa cewa akwai bukatar ya tuna da mutumin da ya fara buda masa hanyar samun na kansa, yace a dalilinsa ne ya zama abin da ya zama a yau.

Gwamnan jihar Benuwai ya ba Mtemave kyautar motar Hilux, ya kuma yi alkawarin ba shi jari, sannan ya ba sauran direbobin kyautan aladu, shanu, kudi da shinkafa.

An nemi a sace mai kudi a Adamawa

Dazu ne aka ji cewa ‘Yan Sanda su na kokarin ceto Bayin Allah da aka dauke a ranar bikin kirismeti a garin Mayo-Belwa, daga cikinsu har da wani jami’in tsaro.

Tsautsayi ya sa ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Jami’in na MOPOL da ya ci kwalliyan kirismeti a jihar Adamawa, 'yan bindigan sun yi tunanin mai kudi aka sungume.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: 'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

Asali: Legit.ng

Online view pixel