Hazikin mutumin Najeriya mai Digiri 7, ya koma makaranta ya yi sabon Digirin PhD

Hazikin mutumin Najeriya mai Digiri 7, ya koma makaranta ya yi sabon Digirin PhD

  • Wani mutumi mai ‘dan karen sha’awar karatun boko, mai suna Temitayo Bello ya yi digirin PhD biyu
  • Dr. Temitayo Bello ya na da digiri a fannin tattalin arziki, ilmin shari’a, aikin banki, da ilmin komfuta
  • Bello ya yi karatunsa ne a jami’o’in Ogun, Osun, Ibadan da Legas, sannan ya fita har kasar Birtaniya

Wani mutumin Najeriya, Temitayo Bello ya kammala karatunsa na digirin PhD, bayan tulin digiri da ya tara a jami’o’in gida da na ketare.

Jaridar Daily Trust ta kawo labarin wannan Bawan Allah, Temitayo Bello, wanda yanzu yana da digiri bakwai a fannoni da dama na ilmi.

Wannan digiri na PhD da Dr. Temitayo Bello ya yi, shi ne na biyu da ya samu a rayuwarsa. Bello ya tara digiri iri-iri da satifiket daga jami’o’i.

Kara karanta wannan

Alkali ya dawo da Birgediya Janar din da aka kora daga gidan Soja shekarun da suka wuce

Bello ya yi digirinsa na uku na zama Dakta ne a bangaren shari’a a jami’ar Ibadan. Kafin nan ya taba yin digirin na PhD, ya kuma zama Dakta.

Rahoton yace digir-digiri din da Bello ya yi a baya a fannin huldar kasashen Duniya da shari’a ne.

Hazikin mutumi
Dr. Temitayo Bello Hoto: www.linkedin.com
Asali: UGC

Daya daga cikin ‘ya ‘yan wannan ‘dan boko, Titilola Bello ya bada sanarwar nan a shafinsa na LinkedIn, yace mahaifinsa ya kammala PhD.

Titilola Bello yace mahaifinsa ya yi digiri da-dama, daga ciki akwai wasu a bangaren ilmin tattalin arziki, aikin banki da ilmin komfuta.

Titilola Bello a LinkedIn

“Wannan kari ne a kan PhD da yake da shi a huldar kasashen Duniya da shari’a, Masters a ilmin shari’a da digirin M.Sc a ilmin tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin

“Da M.Sc a ilmin tattali da aikin banki, M.Sc a ilmin komfuta, digirin LLB da BL a harkar shari’a, da B.Sc a fannin ilmin tattalin arziki.”

Baya ga haka, Bello ya yi digirin farko a tattali da aikin banki da kuma PGD a ilmin komfuta.

Temitayo Bello ya yi karatunsa ne a jami’ar Landan, UNILAG, jami’ar Ibadan, jami’ar aikin gona ta Abeokuta, Babcock da kuma jami’ar jihar Osun.

Yajin-aikin ASUU

Malaman Jami’a sun yi karin haske a game da shirin sake rufe makarantun jami'o'i. Hakan na zuwa ne bayan dogon yajin-aikin da aka yi a shekarar 2020.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Oshodeke yace har yau ba su ji daga bangaren gwamnati ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel