Femi Fani-Kayode ya fadawa Alkali abin da ya raba shi da tsohuwar Mai dakinsa da aka je kotu

Femi Fani-Kayode ya fadawa Alkali abin da ya raba shi da tsohuwar Mai dakinsa da aka je kotu

  • Precious Chikwendu ta nemi a karbe ‘ya ‘yanta daga hannun Femi Fani-Kayode
  • Wannan mata tana ikirarin Fani-Kayode ya hana ta ganin yara hudu da ta haifa
  • Tsohon Ministan harkokin jiragen saman ya karyata duk zargin da ake yi masa

Abuja - Tsohon Ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya nemi kotu ta yi watsi da karar da tsohuwar matarsa, Precious Chikwendu ta shigar.

Femi Fani-Kayode ya maida martani ta bakin lauyoyinsa a babban kotun tarayya na birnin Abuja. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata.

‘Dan siyasar ya fadawa kotu cewa tsohuwar mai dakinsa ta hana ‘ya ‘yan da suka haifa nono da nufin kula da jikinta, ta yadda surarta ba za ta sukurkuce ba.

Sarauniyar kyau ta ki ba yaran da ta haifa mama?

Read also

Iyaye sun fara saida ‘ya ‘yan cikinsu saboda tsabar masifar talauci a kasar Afghanistan

Miss Chikwendu wanda tsohuwar sarauniyar kyau ce, ta kuma ki shayar da ‘ya ‘yan na ta da sunan cewa halin da ta ke ciki ba zai bata damar shayar da yaran ba.

Lauyoyin Fani-Kayode sun shaidawa Alkalin babban kotun cewa ikirarin da Chikwendu take yi na raba ta da ‘ya ‘yanta hudu da karfi da yaji, ba gaskiya ba ne.

Iyalin Femi Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode da Precious Chikwendu da 'ya 'yansu Hoto: www.withinnigeria.com
Source: UGC

“Ta zabi ta bar gidan auren ta ne, ta rabu da ‘ya ‘yan da ta haifa a nan saboda ta samu damar cigaba da sheke aya a waje ba tare da kaidi ba.” – Lauyoyi.
“Ba abin mamaki ba ne don Ms. Precious Chikwendu ta yi gangancin watsi da iyalinta, a lokacin da take tare da ni, ta dauko mutane 12 su kula da yara.”

Read also

CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga

Politics Nigeria ta fitar da rahoto, inda aka ji Lauyan Fani-Kayode yana cewa bayan haka akwai ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan da suke kula da yaransu.

Ba a hana ta ganin 'ya 'yan ta ba - Lauyoyin FFK

“Wanda ta kawo kara ba ta taba yunkurin kula da yaran ba, da sunan cewa tana fama da wani hali da ba zai bari a samu wata alakar ‘ya ‘ya da mahaifiyarsu ba.”
“Ta hana yaran su yi totsi ko su samu madarar jikinta domin ta iya kula da surar jikinta.” - Lauya.

Lauyoyin da suke kare tsohon Ministan sun ce Chikwendu ta fita daga sha’anin yaran cikinta, kuma ba a taba hana ta ganinsu ba, kuma suna magana ta waya.

Za a saida kadarorin Diezani Alison-Madueke

Gwamnatin tarayya ta sa gidaje da gwala-gwalan Diezani Alison-Madueke a kasuwa. Ana zargin tsohuwar Ministar ta tara dukiyoyin ne da satar dukiyar jama'a.

Read also

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Najeriya za tayi gwanjon kayan Alison-Madueke da wasu gidajen tsohon hafsun Najeriya, Marigayi Air Marshal Alex Badeh. Gidajen suna Abuja da Legas.

Source: Legit.ng

Online view pixel