Latest
Jami'an DSS sun kama wani matashi da ya shigo da makamai daga Nijar zuwa Nijar. Matashin ya tsere yayin da sojoji suka nemi kama shi kafin a kamo shi daga baya.
Yayin da ake kai ruwa rana tsakanin APC da Nasir El-Rufai, jigon APC, Joe Igbokwe ya bukaci APC ta daidaita da shi, yana cewa babu Ministan Bola Tinubu da ya fi shi.
Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, ta shirya daukar ma'aikatan lafiya domin bunkasa bangaren lafiya na jihar.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan 'Quranic Festival', shugaban kungiyar Izalah bangaren Kaduna ya yi martani ga Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kalamansa.
Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta ci gaba da sauraron shari'ar almundahana da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta shigar gabanta.
'Yan sanda sun kama barawon da ake zargi da sace kayan masallaci da suka kai N520,000. Barawon ya sace fankoki da tagoggin masallacin ya sayar da su.
Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye sun yi 'yar arangama kan kujerar sakataren PDP na ƙasa a wurin taron ƴan majalisar amintattu watau BoT.
Yayin da ake ci gaba da tababa kan sabon kudirin haraji a Najeriya, an fitar da rahoto kan yankunan da haka fi samar da harajin VAT a shekarar 2024 da ta gabata.
Kamfanin jirgin sama na Max Air ya tabbatar da cewa jirginsa ya samu hatsari a lokacin da ya ke dab da sauka a tashar Malam Aminu Kano,amma ba a samu asarar rai ba.
Masu zafi
Samu kari