Latest
Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N890, inda kamfanin ya bukaci ‘yan kasuwa su bi sahu. Jama’a na jiran ganin ko ragewar za ta kai ga kowa.
Addinin Musulunci ya samu karuwa bayan mata mai suna Fatima ta Musulunta a Kaduna, ta karbi kalmar shahada a hannun Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba da gudunmawar kudi ga iyalan marigayi, Laftanal Kanal Thomas Alari wanda 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe.
Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya yi tsokaci kan ce-ce-ku-ce da ake yi game kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, yana cewa jahilci ne ke haddasawa.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta mika kokon bararta ga 'yan Najeriya. APC ta bukaci 'yan Najeriya da ka da su bari jam'iyyar PDP ta dawo kan mulkin kasar nan.
Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce kwata-kwata bai iya munafurci a siyasa ba kuma ba zai zama kamar yan wasan kwaikwayo a gwamnati ba.
An yi zama a kotu kan tuhumar mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, inda ya bukaci sassauci kan zargin da ake yi masa.
Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya yi kira ga sababbin shugabannin tsaron da aka tura zuwa jihar da su kawo karshen 'yan bindigan da suka addabi mutane.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar kasa (EFCC), Ola Olukoyede ya koka kan halin 'yan Najeriya dangane da cin hanci.
Masu zafi
Samu kari