Latest
Wasu rahotanni sun ce ana hasashen batan tsohon shugaban karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi, Umar Namashaya Diggi bayan wani mummunan harin yan bindiga.
Yan kwadago sun fita zanga zangar nuna adawa da korar ma'aikata sama da 3000 a kamfanin rarraba wuta na Ibadan watau IBEDC, sun gabatar da buƙatu 7.
Jami'ar Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta bayyana alhininta bisa mutuwar ɗalibanta biyar a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su, ta dakatar da karatu.
Atiku Abubakar ya zargi jam'iyyar APC da ƙoƙarin kwace zaɓen Osun da karfi. Ya ce mutanen jihar sun nuna jaruntaka wajen kare dimokraɗiyya daga danniya.
Hatsabibin dan fashi a jihar Zamfara, Gwaska Dankarami, na shirin mika wuya bayan arangama da Sani Dangote inda wasu suka ce ana nemansa ruwa a jallo.
Kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF ta bayyana alhininta bisa rasuwar jagoran PANDEF, Edwin Clark da jagoran Afenifere, Ayo Adebanjo, ta ce kasa ta yi rashi.
'Yan Najeriya masu shiga kasar Nijar da fasfon ECOWAS sun fara fuskantar kalubale da aka fara dakatar da su. Ana zargin ana dawo da wasu zuwa gida Najeriya.
Bayan shafe tsawon lokaci ana rigima kan kujerar sarauta, kotun daukaka kara a Ibadan ta yi zama kan rigimar sarauta a jihar Oyo kan kujerar Soun na Ogbomoso.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara bibiyar kungiyoyi masu zaman kansu dake jihar domin tabbatar da inda suke samun kudin gudanarwa bayan zargin da aka yi wa USAID.
Masu zafi
Samu kari