Latest
Kungiyar 'yan shi'a ta kasa (IMN) ta zargi jami'an tsaron Najeriya da shiga hakkinta ta hanyar hana membobinta gudanar da taro cikin lumana, bayan doka ta basu dama.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya fara aiki a sabon mukamin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta nada shi a hukumar FAAN, ya fadi abin da aka tanada.
Rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar da cewa wani abin fashewa ya jawo gobara a wata kasuwa dake jihar, har ta yi sanadiyyar konewar mutane da dama.
Sanatoci daga Arewacin Najeriya sun ja hankalin gwamnatin tarayya da Bola Tinubu kan titunan Arewa. Sanata Goje da Sanata Sani Musa sun yi kira ga gwamnati.
Majalisar Dokokin Jihar Benue ta dakatar da mambobinta 13 da suka nesanta kansu daga tsige alkalin jihar, mai shari'a, Maurice Ikpambase a zamanta na ranar Talata.
Wani fitaccen malamin addinin kirista, Fasto Sam Alo ya bayyana cewa addu'a ya kamata a rika yi wa shugaban kasa domin Allah ya haska masa hanya mai kyau.
Bayan dan majalisar Amurka ya zargi Hukumar USAID ta tallafawa Boko Haram, Majalisar Dattawa ta kira Nuhu Ribadu da hukumomin DSS da NIA da kuma DIA.
Sheikh Muhammad Bin Usman zai koma limanci a masallacin Kundila na Sahaba bayan rikici da aka yi a masallacin Jami'urrahma. Sheikh Ibrahim Kalil ne ya sanar da haka.
Hon. Mojisola Meranda ta karyata jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ta yi murabus daga muƙaminta saboda wutar rikicin da ta ƙi cinyewa.
Masu zafi
Samu kari