Latest
Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ce suna bin Bello Turji sau da kafa domin kawar da shi. Ana bin diddin dan ta'addar a Zamfara.
Masana sun yi magana kan dalilan da Naira ke kara daraja idan aka kwatanta da dala inda su ke ganin hakan na da alaƙa da matakan da bankin CBN ke ɗauka.
Gwamnatin tarayya ta nada kwamishinonin haraji da za su warware rikici da tabbatar da ba wanda ya kaucewa biyan haraji a Najeriya. Wale Edun ne ya tabbatar da haka.
Binciken gaskiya ya nuna cewa hoton da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta waɓda ke nuna sarkin Musulmi a cikin kayan bokaye kirkirarsa aka yi don yaɗa karya.
Bayan umarnin shugaba Donald Trump kan dokar zama ɗan kasa ga ya'yan yan gudun hijira, Kotun daukaka kara ta ki dage dakatarwar da aka sanya kan umarninsa.
Kwamandan sojin Amurka a Afrika, Janar James Hecker ya ce za su dawo kai farmaki kan Boko Haram da saurann 'yan ta'adda a Afrika domin samar da tsaro.
Watanni da haramta karuwanci da caca a Katsina, hukumar Hisbah ta hana ayyukan gidajen casu domin bin ka'idar addinin Musulunci da kuma al'adar Hausawa.
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya sallami dukkan hadimai da masu rike da sarautar gargajiya a yankunan da ya kirƙiro sababbin masarautu.
Gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 2.3 domin samar da abinci domin ciyar da talakawa a watan Ramadan. Shirin na cikin kokarin gwamna Radda ga talakawa.
Masu zafi
Samu kari