Latest
Naira ta ƙarfafa zuwa 1,494.03/$ a kasuwar hukuma, 1,510.00/$ a kasuwar bayan fage, yayin da CBN ke ci gaba da manufofin kudi don inganta kasuwa.
Daliba daya ta rasu, biyar sun jikkata sakamakon rushewar bangon aji a GGSS Potiskum, Yobe. Gwamnatin jihar ta ce za a binciki musabbabin hatsarin.
'Yan kasuwa da fitattun mutane sun tara wa Ibrahim Badamasi Babangida N17.5bn a yayin taron kaddamar da littafinsa a Abuja. IBB ya yi bayani a wajen taron.
Tinubu ya amince da sabbin jami’o’i a Ekiti da Osun don inganta noma, fasaha da muhalli, tare da bunkasa tattalin arziki da kirkire-kirkire a Najeriya.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce DSS ta kama mai damfara da sunan Izala da Sheikh Kabiru Gombe bayan shafe shekaru yana cutar mutane a jihar Legas.
Wadatar abinci a kasuwanni na ɗaya daga cikin dalilin da suka haddasa karyewar farashi a farkon 2025, gwamnatin tarayyya ta ɗauki matakan da suka taimaka.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki birnin tarayya Abuja, sun yi awon gaba da shugaban ƙungiyar matasan Afenifere na kasa, Eniola Ojajuni.
Jam'iyyar LP na ci gaba da rasa jiga-jiganta ga APC da PDP, ciki har da Valentine Ozigbo, dan takarar gwamna, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a Anambra.
Ministan gidaje, Arc. Ahmed Dangiwa ya ce Katsina za ta sake zaɓen Tinubu da Radda a 2027, yana mai jinjina wa mata da suka fi yawa a rumfunan zaɓe.
Masu zafi
Samu kari