Latest
Bayan gargadin gwamnatin Bola Tinubu kan sake zaben kananan hukumomi, Gwamna Ademola Adeleke ya dage cewa za a gudanar da zaben a Osun a gobe Asabar.
Dakarun sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a sassan Najeriya. Sun kashe yan ta'adda 82, sun ceto mutane 93, sun kwato makamai 86 a hannun 'yan ta'adda.
Bayan hayaniya a majalisar dattawa tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio, an yada bidiyon Akpabio yana korafi kan haka a 2018.
Gwamnatin jihar Kebbi ta fara rabon kayayyakin aure ga ma’aurata 300 a shirin "Auren Gata," domin rage musu nauyin aure da karfafa gwiwar matasa.
Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana cewa babu wani ubangidanda da yake juya shi yadda yake so, ya ce waɗanda ake alaƙanta da shi su taimakonsa suka yi.
Wasu matasa a jihar Borno sun ziyarci wata makabarta da aka tone gawa aka jefa ta cikin ruwa. Ana zargin matsafa ne suka aikata ta'asar. An bukaci daukar mataki.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tuna yadda ya kalubalanci IBB a 1993 bayan lashe zaben Sanata. Tinubu ya ce an yi zaton IBB zai daure shi da ya kalubalance shi.
Jami'an tsaro sun dakile harin masu garkuwa a Sabon Gari Lassa, jihar Borno. Sun cafke mutum uku daga cikin bindigar yayin da aka kwato bindiga kirar gida.
Jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwar cewa jam'iyyarsa ce za ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Masu zafi
Samu kari