Latest
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya ce Bola Tinubu ya taka rawa sosai wajen karya farashin abinci a Najeriya. Ganduje ya ce tsare tsare Tinubu suna aiki.
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana yi martani ga karamin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Abdullahi Ata kan komawarsa kujerar shugaban jam'iyya.
Rundunar sojojin Najeriya ta ba da tabbacin cewa tana ci gaba da aiki tukuru domin ganin cewa ta kawo karshen hatsabibin dan bindiga, Bello Turji.
Sheikh Hayyatullahi ya bukaci Musulmi su kyautata hali, su tsunduma cikin ibada, sadaka, da ciyarwa, tare da neman gafarar Allah domin samun falalar Ramadan.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi martani ga sakon da Bola Tinubu ya tura masa yayin da aka cika mako daya da ranar haihuwarsa ta 61 a duniya.
Direbobin tankunan mai sun dakatar da ɗaukar kaya a Lagos, lamarin da ke barazana ga wadatuwar man fetur da dizal, tare da haddasa fargabar katsewar sadarwa.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina. Miyagun sun hallaka bayin Allah.
Sanata Barau Jibrin ya raba kyautar motoci da babura ga shugabannin APC a jihar Kano. Ya raba motoci 61 da babura 1,137. Ya yi alkawari ga matasa da malamai.
Kungiyar direbobin manyan motoci ta bayyana cewa umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar a kan dakon mai zai rage shigo da fetur Arewa.
Masu zafi
Samu kari