Latest
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta koka kan yadda wasu ke kokarin kawo cikas ga shirin samar da tsaro. Ta yi gargadi kan hakan.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasuwar tsohon gwamna na tsohuwar jihar Oyo, Dr. Victor Omololu Olunloyo, ya ce marigayin ya ba da gudummuwa.
Hukumar dake fafutukar kare hakkin dan adam ta duniya (Amnesty Imternational) ta bayyana rashin jin dadin yadda jami'an yan sanda ke keta hakkin masu zanga-zanga.
Wani matashi, Ibrahim Modibbo ya ce Tinubu bai ci jiharsa ba a 2023, Arewa ta taimaka masa, amma yanzu tana shan wahala. Ya nemi Arewa da Kudu so kada Tinubu a 2027.
Tsohon kwamishina a Ribas, Chisom Gbali, ya bayyana cewa akwai sabuwar makarkashiya da ake shirya wa don tsawaita dokar ta baci da dakatar da gwamna.
Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya yi kra ga Sheikh Sani Yahaya Jingir da Sheikh Abdullahi Bala Lau da su sake haduwa waje daya. Dr Jalo Jalingo ya goyi bayan kiran.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina. 'Yan bindigan sun hallaka mutane tare da raunata wasu daban.
Bangaren Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da batun da kw nuna cewa Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta kwace shugabancin jam'iyyar NNPP daga hannunsa.
Kwamishinan yada labaran Kano, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewa an hada kwamitin da zai karbo diyyar mafarautan da aka kona a Edo.
Masu zafi
Samu kari