Latest
Shugaban sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ba sojojin Najeriya wa'adin wata daya domin murkushe 'yan ta'addan Mahmuda da suka bulla a Arewa.
Gwamnonin kasar nan sun yi ganawar sirri da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa saboda karuwar salwantar da rayuka da Yan ta'adda ke yi a Najeriya.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ce za su yi maraba da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Sokoto. Harin na 'yan bindigan ya kusa ritsawa da shugaban karamar hukumar Tangaza, Isa Kalanjeni.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ka da ya yarda da 'yan siyasa masu sauya sheka zuwa APC.
Yayin da hare-haren yan bindiga ya yi ƙamari, Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro su sauya dabarunsu nan take domin kawo karshen matsaloli a Borno, Benue da Plateau.
Sanata Kawu Sumaila ya tabbatar da cewa ya ajiye NNPP, yayin da ya ƙi bayyana jam'iyyar da ya koma,duk da ana hasashen zai iya faɗawa jam'iyya mai mulki ta APC.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa shugaban karamar hukumar Fufore, a jihar Adamawa, Hon. Shuaibu Babas, ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawar sirri da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa.
Masu zafi
Samu kari