Latest
Hadimin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyana masu masu dora alhaki kan shugaban kasan a matsayin masu saurin manta abubuwan da suka faru.
Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin fara biyan daliban makarantun fasaha N22,500 duk wata bayan yin karatu kyauta. Ministan ilimi ya ce za a rika ba su abinci kyauta.
Gwamnatin Najeriya za ta kafa kotu ta musamman domin maganin dalibai masu satar amsa a lokacin jarrabawa. Ministan ilimi ne ya bayyana haka a Abuja.
Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ya musanta cewa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC, ICPC sun kwato $967.5bn.
Sarkin Epe da ke jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya, Shefiu Ọlatunji Adewale ya kwanta dama yana da shekara 86, za a yi janazarsa yau Asabar.
Wani mutum da matarsa ta haifi 'yan uku a asibitin koyarwa na jihar Kogi ya suma. Mutumin ya ce bai shirya daukar dawainiyar yara 3 a lokaci daya ba.
Wani matashi a jihar Bauchi, Khamis Musa Darazo ya saye ragon layya wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ya sanya wa 'yarsa sunan mamar Tinubu.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya nuna damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ta addabi mutanen Najeriya masu yawa.
Malaman addinin musulunci da ke tawagar NAHCON sun buƙaci mahajjatan Najeriya su yi koyi da Annabi Muhammad (SAW) wajen yi wa ƙasarsu da shugabanni addu'a.
Masu zafi
Samu kari