Latest
A labarin nan, za ji cewa ana zargin jam'iyya mai mulki ta APC da amfani da hukumonin gwamnati wajen tilastawa yan adawa su sadudu tare da komawa cikinta.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince a biya ma'aikata da 'yan fansho kudade don su gudanar da bukukuwan babbar Sallah a cikin walwala da jindadi.
A labarin nan, za a ji cewa jam'iyyar APC ta barranta kanta da rahoton dake cewa ta yiwa dukkanin 'yan majalisu cewa za a ba su takara kai tsaye babu hamayya.
Bayan wasu jiga-jiganta sun karbi muƙami a gwamnatin Agbu Kefas, jam’iyyar APC mai adawa a Taraba za ta hukunta ‘ya’yanta da suka amince ta tayin muƙaman.
Majalisar dokokin jihar Ondo ta yi sauye-sauye don ɗinke eɓaraka a tsakanin shugabanninta, mataimakin kakaki da shugaban marasa rinjaye sun hakura da kujerunsu.
Sanata Abubakar Bello ya ba da N50m ga garin Mokwa da ambaliya ta shafa, yana mai in ta'aziyyar wadanda suka rasu da kuma roƙon Allah ya mayar da asarar da akayi.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da wakilan Tarayyar Turai (EU) domin hadin gwiwa kan ilimi da makamashi. Abba Kabir ya nemi karin hadin gwiwa da EU.
Kungiyar SERAP ta maka kamfanin mai na kasa watau NNPCL a gaban kotu kan yadda kudi N500bn suka ɓata a 2024, ta nemi a fito a yi bayanin inda kuɗin suka makale.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ba zata wajen da ake dafa abincin mahajjatan Kano domin duba ingancin abincin da ake dafa wa 'yan Kano a Saudiyya.
Masu zafi
Samu kari