Latest
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa ta damke akalla mutane 873 bisa zargin karya doka kwanakin da aka gudanar da zanga zanga a jihar, an kai wasu Abuja.
Kimanin mutane bakwai ne 'yan bindiga suka kashe a kauyen Sai da ke jihar Taraba. An ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun yi harin ramuwar gayya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha suka daga wajen manyan yan siyasa da suka hada da Peter Obi, Lukman Salihu da yan kwadago kan zanga zanga.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya fito ya caccaki salon mulkin gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.
Babbar kotun jihar Ribas mai zama a Fatakwal ta rusa kwmaitin rikon kwarya na jam'iyyar APC a jihar Ribas, ta ce an yi kuskure wajen korarar zababbun shugabanni.
Rahoto ya nuna cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi ajalin wani jajurtaccen jami'in sojin Najeriya, Kyaftin Ibrahim Yohana watanni tara kacal bayan aurensa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano ta bankado yadda aka sace kudi N50bn daga asusun jihar aka saye gidaje a biranen Abuja, London da Dubai.
Sanata Buba Shehu na jam'iyyar APC ya yi kakkausan martani ga gwamnan jiharsa, Bala Mohammed, inda ya zarge shi da jawo yunwa da fatara. ga mutanen Bauchi.
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce har yanzun ba a gano musabbabin gobarar da ta ƙona muhimman abubuwa a cocin Redeemed Christian Church of God ba.
Masu zafi
Samu kari