Latest
Rundunar ƴan sanda ta bayyaja cewa ba za ya kyale duk wanda ya yi yunkurin tayar da tarzoma a jihar Kano ba, ta ja kunnen masu shirin ɗauko hayar ƴan daba.
Sheikh Isa Ali Pantami ya tabbatar da karbar mutumin da ya fara tattaki domin zuwa wajensa a Abuja. Ya kuma bayyana cewa idan ya huta za a maido shi Gombe.
Jami'an sojojin Najeriya sun samu nasarr cafke wani soja da ake zargi da sace harsasai 602 a jihar Borno. An cafke sojan ne yana kan hanyar zuwa Kaduna.
Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP) ta yi Allah wadai da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa yadda ya yi jagoranci cikin shekara daya.
Yayin da ake cikin ruɗani umarnin kotuna da suka sha banban, ɗan takarar gwamna inuwar jam'iyyar NNPP a jihar Ogun, Ajadi ya yaba da dawowar Sanusi II.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da motoci 150 da babura 500 domin rabawa ga jami'an tsaro dake yaki da ta'addanci a jihar wanda gwamna Uba Sani ya kaddamar.
Mansurah Isah ya tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jaruman Kannywood, Fati Slow Motion, wadda ta rasu a can kusa da Sudan amma za a yi zaman gaisuwa a Kano.
Wata kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ba da umarnin a fitar sa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, daga fadar Sarkin Kano ta Gidan Rumfa.
Majalisar Dattawa a Najeriya ta yi afuwa ga Sanata Abdul Ningi bayan dakatar da shi na watanni uku inda ta bukaci ya dawo bakin aiki domin ba da gudunmawa.
Masu zafi
Samu kari