Latest
Matan jam'iyyar PDP sun yi zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja suna bukatar a dakatar da shugabar mata ta kasa saboda nuna wariya a shugabancin jam'iyya.
Kwamitin majalisar wakilai kan ma'adanai ya bayyana cewa kasar nan na tafka asarar biliyoyi a bangaren duk shekara wanda ya kai $9bn, shugaban kwamitin ya bayyana.
Majalisar jihar Kano ta gabatar da kudirin samar da sarakuna guda uku masu girman daraja ta biyu da za su ƙasa ƙarƙashin Sarki Muhammadu Sanusi II.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyen Dan Isa dake karamar hukumar Kauran Namoda a Zamfara. Sun kashe mutum hudu tare da sace wasu dari da hamsin.
Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa Hon Ekene Abubakar Adams mai wakiltar mazaɓar Chikun da Kajuru ya riga mu gidan gaskiya ranar Talata.
Sarkin Dawaki Babba, Baffa Dan Agundi ya bayyana kuskuren da aka yi tun farko kan mayar da Sanusi II sarauta inda ya ce shi ba ɗan sarki ba ne domin gadonta ake yi.
Jama'ar karamar hukumar Dawakin Kudu sun shiga tashin hankali bayan an gano gawarwaki guda shida a gidan wani mai sayar da kayan miya, Abdul-Aziz.
Wani jagoran jam'iyyar NNPP a karammar hukumar shanono ya koma jam'iyyar APC a jihar Kano. Sanata Barau Jibrin ne ya karbe shi tare da wasu yan NNPP a Abuja.
Duk da kokarin da babban bankin Najeriya (CBN) ke yi don ganin hada-hadar musayar kuɗi ta daidaita, ƙimar Naira ta kuma faɗuwa kan kowace Dala a ranar Litinin.
Masu zafi
Samu kari