Latest
Malam Uba Sani ya yi ta'aziyya ga iyalan mamba mai wakiltar mazabar Kajuru da Chikun wanda Allah ya yiwa rasuwa da safiyar ranar Talata, 16 ga watan Yuli.
Gwamnatin jihar Abia ta amince da biyan ma'aikatan jihar N15,000 har na tsawon watanni uku saboda mawuyacin hali da ake ciki na kunci da tsadar rayuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar wani dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna. Ya yiwa majalisa da gwamantin Kaduna ta'aziyya.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa bai taɓa ɗaukar ko Naira daga kason kuɗin kananan hukumomin jihar da aka tƴro daga tarayya ba.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar da Gwamna Hope Uzodinma ya samu a zaben gwamnan jihar Imo. Ta yi watsi da karar da jam'iyyun adawa suka shigar.
Sabuwar dambarwa ta bullo a siyasar Kano bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya sake maka shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje a gaban kotu bisa zargin almubazzaranci.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana matakin da ya dauka na koyar da sana'a domin yaki da ta'addanci da samar da zaman lafiya a jihar Katsina.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jin Lagos ya ba kowane matashi mai bautar ƙasa da ya kammala horaswa a yau Talata 16 ga watan Yulin 2024 a jihar N100,000.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce akwai rudani kan hukuncin da kotun tarayya ta yi kan yancin kananan hukumomi, ya kafa kwamiti domin duba hukuncin.
Masu zafi
Samu kari