Latest
Rahotannis sun nuna cewa aƙalla mutane biyar ne suka samu raunuka yayin da ƴan sanda suka sa ƙargi wajen tarwatsa masu zanga zanga a birnin tarayya Abuja.
Wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da Kiristoci ke ba Musulmai kariya a lokacin da suke yin sallar Juma'a ana tsaka da zanga-zanga.
Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya sallami shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar BSIEC daga aiki bayan amincewa da shawarin majalisar dokoki.
Kungiyar Kwadago ta NLC a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadi kan kalaman Gwamna Inuwa Yahaya na jihar kan biyan mafi karancin albashin N70,000.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da ta sanya a fadin jihar a jiya Alhamis domin ba al'umma damar zuwa masallacin Juma'a.
Gwamnatin Borno da hukumomin tsaro sun sanar da sassauta dokar zaman gidan da aka sanya daga karfe 12:00 zuwa 3:00 na rana domin mutane su je masallaci.
Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar da hotuna da kuma bidiyo na yadda masu zanga-zanga ke satar dukiyar jama'a a Kano a ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban karamar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa ya sanya dokar hana fita ta awanni 12 bayan bullar rahoton tashin hankula.
Jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga da suka sake fitowa a babban shataletalen Beger da ke birnin tarayya Abuja, sun harba barkonon tsohuwa.
Masu zafi
Samu kari