Latest
Dan Bello na ganin ya wayar da kan jama’a, wasu su na zargin ya kawo abubuwan da babu tabbas a cikin bidiyoyin na sa har ana kira cewa ya kamata a cafke shi.
Kotun Magistrate da ke jihar Ondo ta daure basarake mai daraja da ake kira Francis Ogundeji a gidan kaso har na tsawon shekaru uku saboda saba umarnin kotu.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa za su cigaba da zama da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso domin dawowa ECOWAS inda ya ce za su inganta tsaro.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya bayyana shirye-shiryen Bola Tinubu kan matasa inda sha alwashin cigaba da tafiya da su a wannan gwamnati.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga har cikin gida, sun yi awon gaba da wani malami, Sheih Isma'il Gausi a Zaria da ke jihar Kaduna da daren ranar Laraba.
An tafka gagarumar asarar rayuka a jihar Kaduna bayan motoci biyu sun yi taho mu gama da juna a Zaria inda mutane 11 su ka rasu nan take, mutum hudu kuma na asibiti.
Rahotanni daga yankin karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sun nuna cewa ɓarayin daji sun hallaka Magajin Garin Gefe da ke yankin Kufana da tsakar dare.
Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta bukaci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da ya janye kalamansa tare da neman afuwar Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan mutuwar tsohon shugaban CAF Issa Hayatou. Marigayi Issa Hayatou ya rike mukaddashin shugaban FIFA.
Masu zafi
Samu kari