Latest
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya fara cika alkawarin da ya ɗaukar wa alkalai na saya masu motocin aiki, ya miƙa masu karin guda 11.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sahalewa hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta rufe asusun kirifton wasu mutane hudu.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin sadarwar zamani, Olusegun Dada, ya lissafa muhimman shirye shirye 11 na gwamnatin tarayya.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ce 'yan damfara sun yi kutse a lambar WhatsApp din gwamnan jihar, Umo Eno inda har suka fara tura sakon neman kudi daga jama'a.
Gwamnan jihar Kebbi ya ce ba a yi maganar dawo da tallafin man fetur ba a zaman majalisar magabatan kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa a ranar Talata.
Gwamnatin jihar Katsina ta janye dokar hana fita gaɓa ɗaya da ta sanya a faɗin kananan hukumomin jihar sakamakon abubuwan da suka faru a lokacin zanga zanga.
Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fito ya caccaki manufofin da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kawo a kasar nan.
Za a ji Sanatan Kano ta Kudu karkashin jam'iyyar NNPP, Kawu Sumaila ya ce yana karbar Naira miliyan 22 a matsayin albashi da kudin gudanarwa a duk wata.
Shugaba kuma jagoran matasa a tafiyar Kwankwasiyya, Abdulrahaman Mai Kadama ya fice daga tafiyar Abba Kabir Yusuf, ya ajiye mukaminsa zuwa APC a Kano.
Masu zafi
Samu kari