Latest
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Manjo Janar M.I Idris mai ritaya a matsayin sabon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar.
Mazauna angwan mai matasa a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa sun kwana da takaicin kisan wani matashin jami'in gwamnati ma kula da shirin Fadama III.
Shugabancin riko na jam'iyyar APC a jihar Ribas ta bayyana wani hadadden shiri na dakile takarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 Daga wani tsagin jam'iyyar.
Tsohon shugaban kasa,Cif Olusegun Obasanjo ya ce ba ya goyon bayan ware wata kabila ko korarsu daga Najeriya, domin kasar ta dukkanin mazauna cikinta ne.
Fitaccen limamin cocin nan, Primate Ayodele ya yi hasashen cewa cikin sauƙi APC za ta sake samun nasara idan PDP ta yi kuskuren bai wa Atiku takara a 2027.
Aaron Uzodike, sabon ɗan majalisar dokokin jihar Abia da aka ba rantsuwar kama aiki a makon nan ya musaɓta cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa Labour Party.
Yan bindiga sun sace dalibai likitoci su 20 a suka fito daga jami'o'in Maiduguri da filato za su tafi Enugu a jihar Benue. Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ta gaji tattalin arzikin kasa a cikin mawuyacin hali daga tsohon shugaba, Muhammadu Buhari duk da jam'iyyarsu daya.
Ana fargabar wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da kwamishinan matasa na jihar Anambra tare da mai ɗakinsa ahanyar zuwa Abuja.
Masu zafi
Samu kari